Hotuna: Jiragen sama biyu sun yi karo a filin jirgin sama na Murtala Muhammed
An samu hargowa tare da kadawar zuciyar jama'a bayan wasu jirage biyu sun yi karo da juna a sashen sauka da tashi na kasa da kasa da ke filin jiragen sama na Murtala Mohammed a jihar Legas.
Wani jirgi A330-243 mai lamba OD-MEA mallakar kamfanin gabas ta tsakiya ya yi karo da wani jirgi 'Boeing 777' mai lamba TC-LJC mallakar kamfanin Turkish.
Wata majiya a filin jirgin ta ce jirgin daukan kaya na kamfanin Turkish ya na ajiye a lokacin da jirgin sama mallakar gabas ta tsakiya ya ci karo da shi.
"Shi jirgin kamfanin Turkish ya na ajiye a 'tarmac' lokacin da jirgin MEA ya zo ya yi karo da shi tare da karya wani bangare na jirgin.
"Jirgin MEA ya na kan titin yin 'gare' kafin tashi sama a lokacin da hatsarin ya faru," a cewarsa.
Tun misalin karfe 12:00 na rana jirgin MEA ke karbar fasinjoji, amma faruwar lamarin ya sa an sauke dukkan fasinjojin da su ka shiga jirgin, a cewar majiyar.
Wata majiya a filin tashin jirgin ta ce jirgin MEA ya na gudanar da kasuwancin jigilar fasinjoji bisa basajar fitar da bakin haure daga Najeriya.
DUBA WANNAN: Tsaka mai wuya: Hukumar CCB za ta gurfanar da Magu
"Wadannan mutanr kasuwancinsu kawai su ke yi ta hanyar fakewa da kwashe bakin haure. Su na zuwa kasar nan a kalla sau uku a sati.
"Jirgin MEA da na kamfanin Turkish su na gudanar da kasuwancinsu ne kawai," a cewar majiyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng