Malabu: Za a dawowa Najeriya da Dala Miliyan 200 na cinikin rijiyar mai - AGF, Malami

Malabu: Za a dawowa Najeriya da Dala Miliyan 200 na cinikin rijiyar mai - AGF, Malami

Ministan shari’an Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya bayyana cewa akwai wasu makudan miliyoyin daloli da gwamnati ta ke jira daga kasashen waje.

Abubakar Malami ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tatso fam Dala miliyan 200 daga cinikin rijiyar man Malabu OPL 245 da aka yi.

Jaridar Daily Trust ta ce babban lauyan na gwamnatin tarayya ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taro da aka shiryawa malaman shari’a domin karawa juna sani.

Rahoton ya ce an yi wannan taro na kwana guda ne a ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja.

Bayan wannan Dala miliyan 200 da za su shigo hannun gwamnatin Najeriya, ministan ya ce sun yi nasarar karbo wasu miliyoyi daga hannun barayin kasar.

Daga cikin kudin satar da Najeriya ta karbe a sakamakon samun nasara a kotu, akwai Naira miliyan 685.7 da wasu Naira miliyan 500 inji AGF, Abubakar Malami.

KU KARANTA: Abin da ya sa mu ke kai wa kasashen makwabta wuta - Najeriya

Malabu: Za a dawowa Najeriya da Dala Miliyan 200 na cinikin rijiyar mai - AGF, Malami
Abubakar Malami SAN
Asali: UGC

Wadannan kudi sun dawo hannun Najeriya ne bayan nasara a shari’a 50 da aka yi a manyan kotun tarayya na kasar wanda a karshe Alkali ya ba gwamnati iko da dukiyoyin.

Daga cikin kotun da gwamnatin tarayya ta samu nasara har da kotun ECOWAS inda aka ba Najeriya iko da wasu Dala miliyan 800 da Naira Miliyan 150 da aka karbe.

A game da kokarin da ma’aikatar shari’a ta yi wajen kare hakkin Bil Adama a Najeriya, ministan ya ce sun biya diyyar Naira miliyan 135 na kisan da aka yi a Apo.

Bayan haka gwamnatin Buhari ta kawo dokar haramta gallazawa Bayin Allah a 2017, tare da yi wa kudirin kafa ma’aikatar Neja-Delta ta NDDC garambawul.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa idan aka yi lissafin abin da zai shiga hannun Najeriya daga cinikin rijiyar man OPL 245, kudin sun haura Naira biliyan 76.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel