'Ba mu yarda ba': APC da PDP sun mayarwa da Mamman Daura martani

'Ba mu yarda ba': APC da PDP sun mayarwa da Mamman Daura martani

Jam'iyyar APC mai mulki da takwararta mai hamayya; jam'iyyar PDP, sun yi watsi da kiran da Mamman Daura, dan uwa shakiki kuma makusancin shugaban kasa ya yi a kan jam'iyyun siyasa su yi watsi da tsarin karba - karba a zaben 2023.

A ranar Talata ne Mamman Daura ya shawarci 'yan Najeriya a kan su zabi dan takarar da ya fi dacewa a zaben kujerar shugaban kasa a shekarar 2023 ba tare da la'akari da yankin da ya fito ba.

Daura ya bayyana hakan ne yayin daya daga cikin daidaikun hirar da ya yi da sashen Hausa na radiyon BBC wacce aka yi ranar Talata a Abuja.

A cewarsa, tunda Najeriya ta gwada tsarin karba - karba har sau uku a baya, zai fi dacewa yanzu jama'a su bawa cancanta fifiko a zaben shekarar 2023, su manta da yankin da mutum ya fito.

Ya ce yin hakan zai inganta hadin kai a cikin kasa.

Sai dai, jam'iyyar APC ta shugaba Buhari ta yi watsi da kiran da Mamman Daura ya yi.

Jam'iyyar ta bayyana hakan ne ta bakin sakatarenta na watsa labarai, Yekini Nabena, yayin wata tattaunawarsa ta wayar tarho da da jaridar Daily Trust.

"Wannan ra'ayin Mamman Daura ne," a cewar Nabena yayin da ya ke bayyana cewa APC za ta cigaba da amfani da tsarin karba - karba a tsakanin bangarorin kasar nan.

'Ba mu yarda ba': APC da PDP sun mayarwa da Mamman Daura martani
Mamman Daura
Asali: Twitter

"Kowa da ra'ayinsa kuma ya na da 'yancin bayyana fahimtarsa, ba wani bakon abu bane, ba kuma abin damuwa bane.

"Jam'iyyar APC, kamar sauran jam'iyyun da ke Najerirya, za ta cigaba da amfani da tsarin karba - karba. Babu wata matsala," a cewar APC.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta gargadi kananan sojoji a kan aiki da 'zugar' su kashe shugabanninsu

Kazalika, ita ma jam'iyyar PDP, ta bakin mataimakin sakatarenta na yada labarai, Diran Odeyemi, ta bayyana cewa ra'ayin Mamman Daura bai shafeta ba.

"Idan lokaci ya yi za mu zauna domin tsara wanne yanki ne zai fito da shugaban jam'iyya da kuma yankin da zai fitar da dan takarar shugaban kasa," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel