Za a bude makarantu a Ranar 4 ga watan Agusta – Gwamnatin Jihar Benuwai

Za a bude makarantu a Ranar 4 ga watan Agusta – Gwamnatin Jihar Benuwai

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnatin jihar Benuwai ta bada sanarwar sake bude makarantun da ke fadin jihar ga yaran da su ke ajin karshe a ajin sakandare.

Gwamnatin Benuwai ta ce za ta bude makarantu a ranar 4 ga watan Agusta, 2020 kamar yadda gwamnatin tarayya ta bada umarni a farkon makon nan.

Kwamishinan harkar ilimi na jihar Benuwai, Farfesa Dennis Ityavyar, ya bada wannan sanarwa a lokacin da ya gana da ‘yan jarida a gidan gwamnati a ranar Talata.

Farfesa Dennis Ityavyar ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya gana da mai girma gwamna Samuel Ortom ranar 28 ga watan Yuli, 2020 a garin Makurdi.

Kafin nan ma’aikatar ilimi ta bada umarnin a bude makarantu saboda masu jarrabawar karshe.

Ma’aikatar ta ce wadanda wannan umarni zai yi tasiri a kansu su ne wadanda ke ajin karshe a karamar sakandare, da babbar sakandare da ajin karshe a firamare.

KU KARANTA: An samu karin mutane 624 dauke da COVID-19

Za a bude makarantu a Ranar 4 ga watan Agusta – Gwamnatin Jihar Benuwai
Gwamnan Jihar Benuwai
Asali: Twitter

Kwamishinan ya ce za a fara jarrabawar WAEC ta kammala sakandare ne a ranar 17 ga watan Agusta, daf da wannan lokaci makarantu za su shirya jarrabawar sharer fage.

Dennis Ityavyar ya ce gwamnati ta dauki matakan da su ka dace na dakile yaduwar cutar COVID-19 a makarantun, ya yi kira ga iyayen dalibai su tanadi takunkumin rufe fuska.

Baya haka, a cewar kwamishinan, gwamna Samuel Ortom ya amince da kafa wani kwamiti da zai yi aikin damka makarantun addinai ga ainihin masu makarantar.

Sakataren gwamnatin Benuwai, Farfesa Anthony Ijohor ne zai jagoranci wannan kwamiti, ana sa ran zai ba gwamnati rahoton aikin da su ka yi nan da mako guda.

Dazu mun ji cewa wasu gwamnonin jihohi sun takaita bude makarantun ga masu shirin jarrabawar WASSCE kawai. Daga ciki akwai jihohin Legas, Ogun da Ekiti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng