'Yan aji 6 kadai za su koma makarantu - Gwamnatocin Legas, Ogun da Ekiti

'Yan aji 6 kadai za su koma makarantu - Gwamnatocin Legas, Ogun da Ekiti

- Gwamnatocin jihohin Legas, Ogun da Ekiti sun ce daliban da za su rubuta jarabawar WASSCE ne kadai za su koma makarantu

- Sun yi wannan bayanin ne a ranar Talata, 28 ga watan Yuli ta bakin kwamishinonin ilimin jihohin

- A ranar Litinin, 27 ga watan Yuli ne Gwamnatin tarayya ta umarci dukkan makarantu a fadin kasar nan su bude don daliban da za a yaye

Gwamnatocin jihohin Legas da Ogun sun ce daliban da ke shirin rubuta jarabawar kammala sakandire wacce hukumar shirya jarabawa ta yammacin Afrika ke shiryawa za su koma makarantu a watan Augusta.

A yayin wannan bayanin a ranar Talata, 28 ga watan Yuli, kwamishinan ilimi na jihar Legas, Folasade Adefisayo da mai bai wa gwamnan jihar Ogun shawara a kan harkar ilimi, Ronke Soyombo, sun bayyana hakan yayin tsokaci a kan komawar daliban makarantu.

Idan za mu tuna, a ranar Litinin, 27 ga watan Yuli ne Gwamnatin tarayya ta sanar sa cewa dukkan makarantun sakandire da ke kasar za su sake budewa a ranar 4 ga Augusta.

A wata takarda da ma'aikatar ilimi ta fitar, ta ce an bai wa daliban makonni biyu don su shirya wa jarabawar WASSCE.

'Yan aji 6 kadai za su koma makarantu - Gwamnatocin Legas, Ogun da Ekiti
'Yan aji 6 kadai za su koma makarantu - Gwamnatocin Legas, Ogun da Ekiti Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Amma a ci gaba mabanbanta a jihohin Legas da Ogun, sun ce jihohin basu yanke shawarar ko za su iya budewa daliban karamar sakandire makarantu ba.

Jihohin Legas da Ogun na daga cikin jihohin da annobar korona ta fi tsamari.

Jihar Legas nada masu cutar har 14,848 yayin da Ogun ke da 1326 kamar yadda hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta bayyana.

A daya bangaren kuwa, Gwamnatin jihar Ekiti ta bi ayarin jihohin Legas da Ogun inda ta ce bata shirya bude sauran azuzuwan ba banda aji shida.

KU KARANTA KUMA: Nasarawa: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5, sun banka wa wasu gidaje wuta

Foluso Daramola, kwamishinan ilimi ta jihar Ekiti, ta bayyana hakan sakamakon annobar korona da tayi katutu a jihar.

A gefe guda, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 624 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:34 na daren ranar Talata 28 ga Yulin shekarar 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel