Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta daure tsohon shugaban sojin saman Najeriya
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta sallama tare da wanke manajan daraktan hukumar sojin sama kuma kwamandan horarwa, Air Vice Marshal Alkali Mohammadu Mamu a kan zargin rashawa da mai shari'a Salisu ke masa a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
A hukuncin alkalai uku na ranar 15 ga watan Yulin 2020, sun yanke wa Mamu hukuncin shekaru 2 a gidan gyaran hali saboda laifi daya cikin hudun da hukumar EFCC ke masa.
Kotun daukaka karar ta wanke shi daga laifuka uku da aka zargesa da su a gabanta.
An kama Mamu da laifin karbar rashawar dala 300,000 ta hannun kamfanin taki na Kalli wanda yake mallakar daya daga cikin 'ya'yansa.
A yayin yanke hukunci, a karar da aka daukaka mai lamba CA/A/788c/2018, JustisYargata Byenchit Nimpar, ta ba Mamu damar biyan tarar N500,000.
Mamu na daya daga cikin manyan hafsin soji da kwamitin shugaban kasa ya zarga da amfani da kujerarsu ba ta yadda ya dace ba.
Kwamitin fadar shugaban kasar an kafa ta ne don bincike kan yadda aka kashe kudin makamai tare da wasu kwangiloli da aka bai wa rundunar sojin.
EFCC ta mika zargi hudu da take wa Mamu a 2016 wanda babbar kotun tarayya da ke Abuja ta karba.
Mai shari'a Garba a wani hukuncin da ya yanke na ranar 29 ga watan Yunin 2018, ya yi watsi tare da wankesa daga zargi hudu da ake masa.
KU KARANTA KUMA: Idan kun isa ku ce kule ku gani a kan yaki da rashawa - Buhari ya yi wa PDP martani
Hakan ya kasance ne saboda rashin bada kwararan shaidu da masu korafi suka yi. Lamarin da yasa lauyan EFCC, Sylvanus Tahir, ya daukaka kara.
Mai shari'a Nimpar ya ga aibin shari'ar tare da yin watsi da Takardar da masu bincike suka bada a kan Mamu don basu bi doka yadda ya dace ba wurin binciken.
Cikin kwamitin kotun harda Justis Abdu Aboki da Justis Emmanuel Akomaye Agim.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng