Buhari ya yi magana a kan zaben Edo da Ondo yayin ganawa da gwamnoni

Buhari ya yi magana a kan zaben Edo da Ondo yayin ganawa da gwamnoni

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yaba da kokarin gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar APC wajen gudanar da zaben fidda 'yan takarar kujerar gwamna a jihar Edo da Ondo cikin nasara.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin magana da gwamnonin jam'iyyar APC a taron da suka gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo a ranar Talata.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya samu damar halartar taron.

"Na ji dadin yadda su ka sauke nauyin da ke kansu tare da daukan matakan da suka dace a kan lokaci," kamar yadda kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya sanar a cikin jawabin da ya fitar.

Taron wanda aka fara da misalin karfe 11:25 na safe, ya samu halartar shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, da sauran gwamnonin jam'iyyar.

An gudanar da taron ne gabanin zaben kujerar gwamna da za a gudanar a jihohin Edo da Ondo wanda za a yi ranar 19 ga watan Satumba, 2020 da ranar 10 ga watan Oktoba, 2020.

Buhari ya yi magana a kan zaben Edo da Ondo yayin ganawa da gwamnoni
Buhari ya yi magana a kan zaben Edo da Ondo yayin ganawa da gwamnoni
Asali: Twitter

Shugaba Buari ya yi amfani da taron wajen nuna jin dadinsa da gamsuwa da aikin kwamitin rikon shugabancin jam'iyyar APC a karkashin jagorancin, Mai Mala Buni.

"Ina jin dadin aikin da shugaban kwamitin riko ya ke yi. Bai zauna ba a kokarinsa na dinke barakar da ta kunno kai a cikin jam'iyya. Ina farin ciki da kokarinsa," a cewar shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: Karramawa: Buhari ya sanyawa tashoshin jiragen kasa sunayen manyan mutne 5

Da ya ke magana amadadin sauran gwamnoni APC, Sanata Atiku Bagudu ya mika sakon godiya ga shugaba Buhari bisa daukan matakan da suka dace wajen warware rigingimun da jam'iyya ta fada

Kazalika, gwamnonin sun yabawa shugaba Buhari a kan daukan matakan dakile barazanar tsaro, inganta tattalin arziki da kuma samun nasarar tsamo Najeriya daga cikin annobar cutar korona.

"Mu na ma su alfahari da shugabancinka da irin nasarorin da ka samu," gwamnonin suka sanar da Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel