MC Tagwaye: Daga neman aron biro a banki na hadu da wanda na aura
A tsakiyar shekarar nan ta 2020 ne shararren mai wasan nan MC Tagwaye ya yi aure. Matashin ya auri Hauwa Uwais ne a ranar 13 ga watan Yuni, 2020.
Matashin ya kan yi wasan barkwanci da sunan shugaban Najeriya, kuma ya shahara saboda irin kamanninsa da kwarewarsa wajen kwaikwayon Muhammadu Buhari.
Jaridar Daily Trust ta yi hira da Sanata MC Tagwaye, domin ta samu labarin yadda ya hadu da ‘Diyar hadimar shugaban Najeriya, Maryam Uwais har su ka yi aure.
Tauraron wanda ainihin sunansa shi ne Obinna Simon ya ce: “Mun hadu ne a cikin banki.”
“Na tambayeta aron biro domin in cika wasu takardu, lokacin da na kare amfani da shi, da gan-gan sai na ki maida mata biron.”
MC Tagwaye ya ce: “Daga nan sai na dumfare ta da cewa ‘kin manta da bironki’, da haka mu ka fara magana, har mu ka karbi lambar wayar juna.”
KU KARANTA: Me Buhari ya fadawa MC Tagwaye da su ka hadu a Katsina

Asali: Twitter
Bisa dukkan alamu daga nan ne kuma alaka ta yi karfi tsakanin su biyu har soyayya ta shiga. Yanzu fiye da wata guda kenan da su ka shiga daga ciki.
Mista Obinna Simon wanda aka fi sani da MC Tagwaye, ya ce a lokacin da ya hadu da sahibarsa ba ta san ko wanene shi ba, har sai da tafiya ta yi tafiya.
Shekaru goma da su ka wuce, MC Tagwaye malamin makaranta ne mai koyar da ilmin kimiyya da aikin gona, daga nan ya shiga harkar barkwanci da magana a taro.
Bayan haka, MC wanda Ibo ne da ya yi zaman garin Ingawa a Katsina ya na noma, kuma ya kan yi kasuwanci kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.
Mahaifiyar amaryarsa ita ce Maryam Uwais, MFR wanda ta na cikin masu ba shugaban Najeriya shawara. Mahaifin ta shi ne tsohon Alkalin alkalai, Muhammad Uwais.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng