Kebbi: Kotu ta bai wa ma'aikacin banki masauki a gidan yari bayan luwadi da yaro karami

Kebbi: Kotu ta bai wa ma'aikacin banki masauki a gidan yari bayan luwadi da yaro karami

Wata kotun majistare ta hudu da ke zama a Birnin Kebbi, ta bukaci a adana mata wani ma’aikacin banki mai suna Hussaini Sahabi a gidan gyara hali.

Ana zargin matashin mai shekaru 25 da yin luwadi da wani yaro mai shekaru 10, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda aka shigar da karar, an zargi matashin mai aiki da wani banki a jihar da lalata karamin yaron.

An gurfanar da ma’aikacin bankin a ranar 21 ga watan Yulin 2020.

Kebbi: Kotu ta bai wa ma'aikacin banki masauki a gidan yari bayan luwadi da yaro karami
Kebbi: Kotu ta bai wa ma'aikacin banki masauki a gidan yari bayan luwadi da yaro karami Hoto: Thisday
Asali: Twitter

Dan sanda mai gabatar da kara mai suna Muntari Mati, ya sanar da kotun cewa, wanda ake zargin mazaunin kwatas din Gwadangwaji ne da ke cikin Birnin Kebbi. Ya aikata laifin ne a gidansa.

KU KARANTA KUMA: DSS: Wasu fitattun 'yan Najeriya na shirin hargitsa kasar nan

Ya ce laifin ya ci karo da sashi na 284 na dokokin jihar.

Alkalin kotun, Aminu Diri, ya dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Augusta. Ya bukaci a adana masa wanda ake zargin a gidan gyaran hali.

A wani labari na daban, wani mutum mai shekaru 46 ya shiga hannun 'yan sanda sakamakon fyade da yayi wa yarinya mai shekaru 13.

Wata kotun majistare da ke Makurdi ta bukaci a adana shi a gidan yari.

Wanda ake zargin mai zama a lamba 54 titin Bauchi da ke yankin Wadata da ke Makurdi, ana zargin ya aikata laifin ne yayin da aka tura yarinyar tallan gyada.

Dan sanda mai gabatar da karar ya sanar da cewa, wani Abdulrazak Unuru da ke lamba 7 a titin Ejule a Wurukum da ke Makurdi ya kai wa 'yan sandan korafi a ranar 7 ga watan Yulin 2020 wurin karfe 9 na safe.

Ya ce ya tura diyarsa mai shekaru 13 tallan gyada amma a kan hanyarta ta zuwa mutumin ya ja ta da karfi zuwa cikin dakinsa inda yayi lalata da ita.

Bayanan sirri sun tabbatar da cewa an kama Alhaji Sani Hashimu a kan laifin wanda ya ci karo da sashi na 284 na Penal Code.

Amma kuma wanda ake zargin ya musanta laifin da ake zarginsa da shi.

A lokacin da aka kira shari'ar, Alkalin ya ki karbar duk wani roko.

Ya bukaci a ci gaba da bincike sannan a adana wanda ake zargin a gidan gyaran hali zuwa ranar 9 ga watan Oktoba 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng