DSS: Wasu fitattun 'yan Najeriya na shirin hargitsa kasar nan

DSS: Wasu fitattun 'yan Najeriya na shirin hargitsa kasar nan

- Hukumar DSS ta yi zargin cewa wasu shahararrun mutane a kasar na kokarin kawo rashin zaman lafiya a kasar

- DSS ta ce wadannan mutane sun kirkiri hanyoyin aiwatar da mugun nufinsu ta yin kalamai da za su tunzura jama'a, kungiya da kabilun kasar

- Sai dai ta jadadda cewa jami'anta na aiki da sauran jami’an tsaro don tabbatar da cewa wadannan mutanen basu cimma manufarsu ba

- Kakakin hukumar, ya ce duk dan kasa mai bin doka tare da son ganin zaman lafiya ya sanar da duk al’amuran ta’addanci da ya ga wani ko wata kungiya suna aikatawa

Hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta ce wasu fitattun mutane na kokarin hargitsa wasu sassa na kasar nan.

A wata takarda da ta fita a ranar Litinin, Peter Afunanya, kakakin hukumar DSS, ya ce wadannan fitattun mutanen sun kirikiro wasu hanyoyi da suka hada da yin kalamai da zai tunzura jama’a, kungiyoyi da kabilu a fadin kasar.

Afunanya ya ce ‘yan sandan farin kayan na aiki da sauran jami’an tsaro don tabbatar da cewa wadannan mutanen basu cimma manufarsu ba, jaridar The Cable ta ruwaito.

DSS: Wasu fitattun 'yan Najeriya na shirin hargitsa kasar nan
DSS: Wasu fitattun 'yan Najeriya na shirin hargitsa kasar nan Hoto: Politics Nigeria
Asali: UGC

“Hukumar na sane da su, tsarinsu da kuma masu daukar nauyinsu. A saboda haka, ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani yunkuri na karya doka a fadin kasar nan ba,” yace.

“A sakamakon haka, hukumar na aiki tare da sauran hukumomin tsaron wurin tabbatar da cewa an bi doka tare da cimma burin zaman lafiya.

“Hukumar ta jaddada kokarinta na ganin wanzuwar zaman lafiya a cikin gida Najeriya, kuma za ta yi duk abinda ya dace wurin hukunta masu kokarin tada fitintinun cikin gida.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaban PDP ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya na dan lokaci

Kakakin hukumar, ya ce duk dan kasa mai bin doka tare da son ganin zaman lafiya ya sanar da duk al’amuran ta’addanci da ya ga wani ko wata kungiya suna aikatawa.

Har dai a halin yanzu, ba a san wacce kungiya bace ko kuma wadanne mutane bane Afunanya ke nufi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel