Yanzu Yanzu: Shugaban PDP ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya na dan lokaci

Yanzu Yanzu: Shugaban PDP ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya na dan lokaci

- Jam’iyyar Peoples Democratic Party na alhinin rashi na wani babban mambanta

- Shugaban babbar jam’iyyar adawar na jihar Abia ya rasu

- Johnson Onuigbo ya mutu a ranar Litinin, 27 ga watan Yuli, bayan ya yi fama da rashin lafiya na dan lokaci kadan

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shiga alhini sakamakon mutuwar shugabanta na jihar Abia, Johnson Onuigbo.

A bisa ga kafar labarai ta TVC, Onuigbo wanda aka fi sani da Akinboard ya mutu a daren ranar Litinin, 27 ga watan Yuli, bayan ya yi fama da rashin lafiya na dan kankanin lokaci. An ajiye gawarsa a wajen ajiyar gawa a wani asibiti a Umuahia.

Yanzu Yanzu: Shugaban PDP ya rasu bayan rashin lafiya na dan lokaci
Yanzu Yanzu: Shugaban PDP ya rasu bayan rashin lafiya na dan lokaci Hoto: TVC
Asali: UGC

A wani rahoton AIT, wata majiya da ta zanta da kafar labaran a kan sharadin boye sunanta, tace ba a san musababbin mutuwar Onuigbo ba.

KU KARANTA KUMA: PDP ta bayyana dalilin da yasa Dogara ya koma APC

Marigayin ya jagoranci kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar bayan an rushe kwamitin shugabancin jam’iyyar adawar reshen jihar Abia.

A wani labari na daban, yan bindiga sun kashe wani lauya mazaunin Kaduna, Haro Gandu, yayin da suka yi garkuwa da matarsa da kuma yaronsa, a gidansa da ke Tollgate, karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Gandu ya kasance ma'aikaci ne a ma'aikatar shari'a, an kashe ni bayan da 'yan bindigan suka afka gidansa a daren ranar Lahadi.

Timothy Gandu, tsohon kwamishin tsara tattalin arziki, kuma dan uwan mamacin, ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin.

A cewarsa, 'yan bindigar sun shiga gidan ne da karfin tsiya bayan da suka balle daya daga cikin tagogin gidan.

Tsohon kwamishinan ya ce 'yan bindigar sun fara harbin kaninsa ne a kafada, a lokacin da yayi kokarin guduwa kuma suka harbe shi a baya.

Gandu ya ce bayan da aka kashe shi, 'yan bindigar suka tafi da matarsa da yaronsa.

Ya ce, "Sunzo gidan ne a daren ranar Lahadi, suka balle taga daya sannan suka shiga gidan.

"Sun fara harbin kafadarsa, ya yi kokarin mutuwa, suka bishi, suka harbe shi a baya, a nan take ya mutu. Sun yi awon gaba da matarsa da yaronsa.

"Kusan dai labarin ta'addancin da ke faruwa ke nan a ko ina. Yan bindiga na shiga gidaje suna kisa da garkuwa da jama'a."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng