COVID-19: Fayemi da wadanda su ka harbu su na kara samun sauki - Kwamishina

COVID-19: Fayemi da wadanda su ka harbu su na kara samun sauki - Kwamishina

An gano cewa wasu daga cikin majalisar kwamishinonin mai girma Dr. Kayode Fayemi na jihar Ekiti sun harbu da kwayar cutar COVID-19.

A ranar Lahadi ne kwamishinan harkar shari’a na Ekiti, Wale Fapohunda ya tabbatar da cewa ya yi gwajin kwayar cutar, kuma sakamakon ya nuna ya kamu da COVID-19.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa bayan babban lauyan na gwamnatin Kayode Fayemi, akwai wasu kwamishinonin da su ke jinyar wannan cuta a halin yanzu.

Kwamishinar kiwon lafiya ta Ekiti, Dr. Mojisola Yaya-Kolade ta tabbatar da cewa Wale Fapohunda ya kamu da cutar, haka kuma akwai wasu mukarabban gwamnatin.

Sai dai ba a bayyana sunayen sauran kwamishinonin da su ke dauke da Coronavirus ba.

Mojisola Yaya-Kolade ta ce a matsayinta na likita, ya sabawa dokar aiki ta bayyanawa jama'a sunayen masu jinyar COVID-19.

KU KARANTA: COVID-19: Jami'an Gwamnati sun yi bindiga da Biliyan 1.7

COVID-19: Gwamnan Ekiti da wadanda su ka harbu su na kara samun sauki
Kayode Fayemi Hoto: Gwamnan Ekiti
Asali: Twitter

Kwamishinar ta ce: “Wadanda su ka kamu da cutar su na da damar su fito su sanarwa Duniya da kansu cewa sun kamu da cutar.”

“Kamar yadda ku ke da labari, ministan shari’a ya sanar da halin da ya ke yi ciki ta kafar Twitter, ina fada maku cewa akwai wasu kwamishinoni a gwamnati da su ke dauke da cutar.”

“Amma dole in ce su na da damar su sanar da halin da su ke ciki ko kuma su yi gum saboda sanannun dalilai.” Yaya-Kolade ta fadawa ‘yan jarida.

A jihar Ekiti yanzu akwai mutane 67 da su ke dauke da COVID-19 kamar yadda kwamishinar ta bayyanawa manema labarai.

“Duka masu jinyarmu su na warkewa. Su na samun sauki kuma ba mu samun matsala da su.”

Idan ba ku manta ba kwanaki Gwamna Fayemi ya sanar da cewa ya gano ya na dauke da kwayar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng