Rundunar 'yan sanda ta saka dokar ta baci a jihar Kaduna

Rundunar 'yan sanda ta saka dokar ta baci a jihar Kaduna

Babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF), IGP Mohammed Abubakar Adamu, ya bayar da umarnin gaggauta saka dokar ta baci a ilahirin kudancin jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sanda ta fitar a shafinta na tuwita a yau, Litinin, ta bayyana cewa IGP Adamu ya bukaci jama'a su bawa jami'an tsaro hadin kai da goyon baya.

A cewar rundunar 'yan sanda, saka dokar ta bacin ya zama tilas domin samun damar shawo kan rikicin da ake fama da shi a wasu sassan kudancin jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa IGP Adamu ya umarci kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna da ya tabbatar da kaddamar da dokar da karfinta.

Kazalika, an bukaci kwamishinan ya yi amfani da jami'an rundunar 'yan sanda na musamman da aka turo zuwa kudancin jihar Kaduna domin tabbatar da kare lafiya da dukiyoyin jama'a.

An dorawa kwamishinan alhakin tabbatar da cewa ya yi amfani da rundunonin 'yan sanda na musamamman domin ganin an samu dawowar zaman lafiya mai dorewa a cikin jama'a da tsakanin makwabtan kabilu da garuruwansu.

Rundunar 'yan sanya ta saka dokar ta baci a jihar Kaduna
IGP M. A. Adamu
Asali: Facebook

Daga cikin rundunonin tsaro na musamman da aka tura domin tabbatar da zaman lafiya a yankin kudancin jihar Kaduna sun hada da; PMF (Police Mobile Force), CTU (Counter Terrorism Unit), jami'an leke sirri, jami'ai na musamman, rundunar sojoji da sauran jami'an hukumomin tsaro.

DUBA WANNAN: An samu zaman lafiya a Najeriya idan aka kwatanta da shekaru 5 baya - Buratai

"IGP ya na mai mika sakon ta'aziyya da jaje ga dukkan jama'ar jihar Kaduna, musamman wadanda suka rasa wani nasu ko kuma suka yi asarar dukiya.

"Ya bawa jama'a tabbacin cewa rundunar 'yan sanda za ta za ta yi amfani da kwarewa da duk wani iko da karfi da doka ta bata domin ganin an samu dawowar zaman lafiya a sassan da abin ya shafa," a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa IGP Adamu ya gargadi ma su aikata laifi da karya doka su rufawa kansu asiri su tuba, su daina miyagun aiyuka ko su fuskanci fushi da ikon doka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel