Kwankwasiyya ta nemi kotu ta dakatar da Ganduje daga karbar rancen N300bn daga kasar China

Kwankwasiyya ta nemi kotu ta dakatar da Ganduje daga karbar rancen N300bn daga kasar China

Babbar darikar siyasar nan ta Kwankwasiyya, ta maka gwamnan jihar Kano a kotu dangane da shirinsa na karbo rancen Yuro 684,100,100 daga wani babban banki na kasar China.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kulla aniyyar karbo bashi wannan kudi da sun kai kimanin Naira biliyan daga kasar China, domin aiwatar da aikin shimfida layin dogo mafi gudu a jihar Kano.

A dalilin haka darikar Kwankwasiya ta yi wani dogon rubutu na korafi da kalubalantar wannan yunkuri da gwamna Ganduje ke shirin yi, wanda a cewarta ba a biyo da shi ta hanyar da ta dace ba kuma ya sabawa ka'ida.

Kwankwasiyya ta rubuta takardar mai dauke da korafi tare da kalubalantar gwamnatin jihar Kano da kuma majalisar dokoki ta jihar kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Darikar wadda ta kasance mai jan gayya a jihar Kano da kuma wasu jihohin Najeriya musamman na Arewa, ta aike da takardar mai dauke da kokr zuwa ga shugaban majalisar dattawa da ma'aikatar kudi ta Najeriya.

Madugun Kwankwasiyya; Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Madugun Kwankwasiyya; Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Asali: UGC

Haka kuma wasikar tana jan hankalin ofishin jakadancin China a Najeriya, Ofishin kula da bashi na fadar shugaban kasa da kuma Bankin Raya kasar China wanda gwamnan ke shirin karbo rancen a wurinsa.

A sanarwar da Aminu Abdussalam, mataimakin dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar PDP a zaben 2019 ya fitar, ya kirayi dukkanin masu ruwa da tsaki da tashi tsaye wajen ganin wannan lamari bai tabbata ba.

Ya ce wannan makudan kudin idan aka bari Gwamna Ganduje ya yi ido biyu da su, to kuwa "babu a inda za su kare sai a aljihun babbar rigarsa."

Yake cewa, kudin da Gwamnan yake shirin karbo wa bashi shi ne kwatankwacin kudaden shiga da jihar ta samu a tsawon shekaru 15 da suka gabata.

KARANTA KUMA: Covid-19: FOA ta fidda kasashe 27 da za su fuskanci matsalar karanci abinci

Sanarwar ta bayyana takaicinta a kan yadda gwamnatin Kano ke kalace-kalace manyan da suka bukatar biliyoyin nairorin wajen aiwatarsu a yayin da ake ci gaba da fama da mummunan tasirin da annobar korona ta haifar.

Wannan lamari matukar aka bari ya tabbata kamar yadda Honarabul Abdussalam ya bayyana, babu abin da zai haifar face mummunar barazana da kuma zagon kasa ga makomar sashen ilimi, da na lafiya a jihar.

Ya ce jihar Kano tana iya shafe fiye da tsawon shekaru 50 kafin ta iya biyan bashin da gwamnan ke shirin karbo wa.

A karshe sanarwar ta kuma bayyana damuwa kan yadda gwamnatin jihar ta gaza kawo ingantaccen daidaito a sashen ilimi, lafiya da yaki da talauci amma ta bige kan ayyukan da suke kasa ta fuskar bukata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel