Da duminsa: FG ta tsayar da ranar bude makarantun sakandire a cikin watan Agusta

Da duminsa: FG ta tsayar da ranar bude makarantun sakandire a cikin watan Agusta

Gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da cewa za a bude makarantun sakandire a fadin kasa domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar zana jarrabawar kammala karatun sakandire (WASSCE).

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta fitar a yau, Litinin, ta bayyana cewa za a bude makarantun ne daga ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2020.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ben Bem Goong, darektan yada labarai na ma'aikatar ilimi ta kasa.

A cewar sanarwar, an yanke shawarar bude makarantun ne bayan masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi sun shafe lokaci mai tsawo suna tattaunawa a ranar Litinin.

Daliban da ke aji shidda; watau shekarar karshe, da takwarorinsu da ke aji uku ne kawai zasu koma makaranta, a cewar sanarwar.

Da duminsa: FG ta tsayar da ranar bude makarantun sakandire a cikin watan Agusta
Ministan Ilimi; Adamu Adamu
Asali: Twitter

"Za a bude makarantn sakandire daga ranar 4 ga watan Agusta, 2020, ga daliban ajuzuwan da zasu rubuta jarrabawar kammala makaranta. Hakan zai bawa dalibai damar yin amfani da sati biyu domin yin shirin jarrabawar WAEC, wacce za a fara ranar 17 ga watan Agusta," a cewar sanarwar.

DUBA WANNAN: An samu zaman lafiya a Najeriya idan aka kwatanta da shekaru 5 baya - Buratai

"An cimma wannan matsaya ne bayan gudanar wa wani muhimmin taro da ma'aikatar ilimi ta tarayya, kwamishinonin ma'aikatun ilimi a jihohi 36, kungiyar malamai ta kasa (NUT), ma su makarantu ma su zaman kansu da wakilan hukumomin tsara jarrabawa.

"Yayin taron, wanda aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo, an amince a kan cewa za a bude makarantun a ranar 4 ga watan Agusta, jim kadan bayan kammala bukukuwan babbar Sallah," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel