Dalilin da ya sa 'yan majalisar dattawa suka ki bari a san albashin da suke dauka - Wani Sanata ya fasa kwai

Dalilin da ya sa 'yan majalisar dattawa suka ki bari a san albashin da suke dauka - Wani Sanata ya fasa kwai

Shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan al'amuran shari'a da hakkin dan Adam, Sanata Michael Opeyemi Bamidele, ya ce wasu bukatun na taka rawar gani wurin kawo rashin fahimta tsakanin majalisar tarayya karo ta tara da 'yan Najeriya.

Ya kara da cewa, wasu daga cikin abokan aikinsa suna sukar wallafa albashinsu tare da alawus saboda tsaron kasa.

Jama'ar kasa na ta cece-kuce a kan albashi tare da alawus din 'yan majalisar tarayya. Da yawa kuwa na ta kira ga gwamnati a kan ta zabtare shi.

A shekarar da ta gabata, wasu 'yan majalisar suna ta mika bukatun da suka janyo cece-kuce.

Wasu daga cikin bukatun sune na daidaita kafafen sada zumuntar zamani, hana kalamun kiyayya, kafa cibiya don tubabbun 'yan ta'adda, bukatar hana amfani da janareto da sauransu.

Dalilin da ya sa 'yan majalisar dattawa suka ki bari a san albashin da suke dauka - Wani Sanata ya fasa kwai
Dalilin da ya sa 'yan majalisar dattawa suka ki bari a san albashin da suke dauka - Wani Sanata ya fasa kwai Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A yayin zantawa da manema labarai a ranakun karshen mako a Abuja, Sanata Bamidele dan jam'iyyar APC mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, ya ce wadannan bukatun 'yan Najeriya basu fahimcesu ba.

KU KARANTA KUMA: Ibrahim Magu ya kara shiga matsala: DSS na neman takardar bayyana kadarorinsa daga CCB

"A shekara daya da ta gabata, mun mika wasu bukatun da suka kawo cece-kuce duk da sanatocin da suka mika bukatun suna yi wa kasa fatan alheri ne.

"Amma kuma da yawa daga cikin jama'a basu fahimta ba. Idan dan majalisa ya mika bukata gaban majalisa a karon farko, bai kamata a yi caa a kan 'yan majalisar ba.

"Bayan 'yan majalisar sun yi muhawara a kan bukatar, za a bai wa jama'a damar kalubalanta. Ana iya samun lokacin da anan take za a kashe bukatar kuma ta tafi kenan.

"Amma kuma sau da yawa ana duba irin bukatar ne tun farko kafin a karanto ta ga majalisar sannan a sako ta ga jama'a. sau da yawa suna fatan alheri."

Ya ce yana ta mika bukatar a wallafa albashin 'yan majalisa da alawus din su don jama'a su sani amma wasu daga cikin 'yan majlsar basu amince ba saboda tsaron kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel