Musulmai sun koka a kan kisan mummuke da ake masu a Kudancin Kaduna

Musulmai sun koka a kan kisan mummuke da ake masu a Kudancin Kaduna

Gidauniyar matasan addinin Musulunci na kudancin Kaduna (MYFOSKA), sun yi zargin yawan kashe-kashen mambobinsu wadanda ke hanyar tafiya ko wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullun a kudancin Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yankunan kudancin Kaduna na fama da kashe-kashe daga ‘yan bindiga da kuma hare-haren ramuwar gayya tsakanin manoma da makiyaya.

Harin baya-bayan nan shine na Zikpak wanda ya yi sanadiyar kisan mutum tara a karamar hukumar Jama’a.

Musulmai sun koka a kan kisan kiyashin da ake masu a Kudancin Kaduna
Musulmai sun koka a kan kisan kiyashin da ake masu a Kudancin Kaduna
Asali: UGC

Sai dai, a wani jawabi daga MYFOSKA dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Mohammed Kabir Bello, ya bayyana cewa Musulmai sun tsinci kansu a tsakanin hari da kisan mummuke a yankuna daban-daban na kudancin Kaduna.

A duk lokacin da aka ji jita-jitan kowani irin hari a yankin, Musulmai abun ke shafa, sai a toshe hanyoyi kuma duk Musulmin da ke hanya sai a kashe shi,” in ji shi.

Kungiyar ta ce an kai wa mutum biyar harin bazata sannan aka kashe su a watan Yuli, ciki harda tsohon sakataren hakimin Dangoma, Sallau Musa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na bar PDP, na koma APC - Dogara

An kashe shi ne a kan hanyarsa ta zuwa Dangoma daga Kafanchan a ranar 22 ga watan Yulin 2020.

“Gaba daya an kashe sama da mutum 100 a yayinda suke kan hanyar tafiya tun daga 2016,” in ji kungiyar.

A baya mun ji cewa an kashe mutane tara a wani harin da aka kai kan al’umman Zipkak da ke karamar hukumar Jama’a na jihar Kaduna.

Yankin Jama’a na daga cikin kananan hukumomin da gwamnatin Kaduna ta sanya dokar kulle na sa’o’i 24 saboda rashin tsaro amma duk da haka aka ci gaba da kai hare-hare.

An tattaro cewa ‘yan bindiga sun far ma kauyen, wanda ya ke kimanin rabin kilomita daga Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jama’a, da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Juma’a.

Gideon Mutum, wani mazaunin yankin, ya ce kimanin kwanaki uku da suka gabata, an yada jita-jitan cewa za a kawo hari amma ba a tsaurara matakan tsaro ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel