Kwamitin da su ka jefa Magu a matsala sun yi dace da manyan ayyukan Gwamnati

Kwamitin da su ka jefa Magu a matsala sun yi dace da manyan ayyukan Gwamnati

Alamu sun nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yanke shawarar yin waje da Ibrahim Magu daga hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa.

Jaridar Vanguard ta ce mai girma shugaban kasar ya na nuna cewa kwanakin Ibrahim Magu sun kare a EFCC, duk da bai furta komai tun da aka soma binciken shugaban na EFCC ba.

Rahoton ya ce yardar da shugaban kasar ya yi wa Magu ta zagwanye, har ta kai an dakatar da shi daga mukamin da ya ke kai na mukaddashin shugaban hukumar EFCC na kasa.

Ganin yadda kwamitin PACRA da shugaban kasa ya kafa domin binciken kadarorin sata ya hadu a kan zargin Magu da aikata laifi ya sa Buhari ya karaya da sha’anin shugaban na EFCC.

Kwamitin PACRA ya yi aikinsa na tsawon watanni hudu, inda ya zargi Magu da aikata ba daidai ba, duk ba tare da mukaddashin shugaban EFCC ya samu labari ba.

Olufemi Dominic Lijadu da Mohammed Nami ne su ka jagoranci wannan aiki a 2018 tare da Gloria Bibigha.

KU KARANTA: Akpabio ya cirewa Sanatoci zani a kasuwa kan zargin cin kudin NDDC

Kwamitin da su ka jefa Magu a matsala sun yi dace da manyan ayyukan Gwamnati
Ibrahim Magu Hoto: EFCC/Twitter
Asali: Facebook

Bayan karbar rahoton aikin na su Lijadu da Mohammed Nami, shugaba Buhari ya yi alkawarin zai dauki mataki bisa shawarwarin da su ka bada domin magance satar dukiyar kasa.

Ganin irin aikin da su ka yi, shugaba Buhari ya ba ‘yan wannan kwamiti aiki a gwamnatinsa. Olufemi Dominic Lijadu shi ne ya zama sabon shugaban hukumar nan ta SEC.

Shi kuma sakataren kwamitin binciken, Mohammed Nami ya gaji Babatunde Fowler a hukumar FIRS mai karbar haraji a Najeriya.

Ita kuwa Gloria Bibigha wanda ita kadai ce macen da ke cikin kwamitin ta samu aiki ne a ofishin babban Akanta na gwamnatin tarayya, damaBibigha ta kware wajen binciken kudi.

Vanguard ta ce a sakamakon aikin wannan kwamiti ne aka jefi Magu da zargin laifuffuka da su ka hada da rashin da’a, kawo tasgaro wajen wasu bincike da kuma azurta kansa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel