Korona: Sabbin mutane 555 sun kamu a Najeriya, Kano ta dawo mataki na biyu
Kamar yadda Legit.ng Hausa ke kawo maku rahotanni daga hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa (NCDC) a kan annobar COVID-19, a yau Lahadi, 26 ga watan Yulin 2020, hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, sabbin mutane 555 sun kamu da cutar korona a fadin Najeriya.
Alkaluman na ranar Lahadi sun nuna cewa jihar Kano ta biyo bayan jihar Legas a yawan adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar korona a ranar Lahadi.
A cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta bayyana jimilllar mutanen da suka kamu da kwayar cutar korona a kowacce jiha kamar haka;
Sabbin mutane 555 sun kamu da annobar korona a Najeriya
Lagos-156
Kano-65
Ogun-57
Plateau-54
Oyo-53
Benue-43
FCT-30
Ondo-18
Kaduna-16
Akwa Ibom-13
Gombe-13
Rivers-12
Ekiti-9
Osun-8
Cross River-3
Borno-2
Edo-2
Bayelsa-1
Ya zuwa karfe da 10:48 a daren ranar Lahadi, jimillar mutane 40,532 aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar korona a Najeriya.
An sallami mutane 17,374 daga cikin adadin mutanen da suka kamu da cutar bayan an tabbatar da samun saukinsu, sannan cutar ta kashe mutane 858 a fadin Najeriya.
DUBA WANNAN: Yakin neman zabe: An yi musayar wuta tsakanin magoya bayan APC da PDP a Edo
A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wani bene mai hawa biyu da ake ginawa a Abuja ya rushe tare da ritsawa da mutane 10 da kuma yi wa wani mutum guda mummunan rauni.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a bayan kasuwar zamani da ke unguwar Dawaki a yankin Galadima a birnin tarayya, Abuja.
Lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 10:40 na safe, ya yi sanadiyyar raunata leburorin da ke aiki, wadanda kuma sune mazauna benen..
Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da takwarorinsu na birnin tarayya (FEMA) sun gaggauta zuwa wurin tare da tserar da mutanen bayan an sanar dasu.
An garzaya da mutum guda da ya samu mummunan rauni tare da wasu mutane biyu zuwa asibiti mafi kusa.
Idris Abbas, babban darektan FEMA, ya ce basu bata lokaci ba wajen aika jami'ansu bayan samun labarin rushewar benen ta hanyar kiran lambobin wayarsu na 'ko ta kwana'.
Ya bayyana cewa tun asali akwai gini a wurin, amma sai mai wurin ya yanke shawarar mayar da shi bene.
"Lamarin ya ritsa da mutane 10, an kubutar da mutane uku sannan an garzaya dasu zuwa asibiti," a cewarsa.
Kazalika, ya gargadi masu gidaje da kangwaye su guji saba ka'idar yin gine - gine wacce hukumar raya birnin Abuja ta tsara.
Abbas ya kara da cewa hukuma ta dakatar da maigidan daga aikin dora bene a kan tsohon gidansa amma ya yi kunnen kashi, ya zabi a yi masa aiki yayi hutun karshen mako.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng