Dalilin da yasa na bar PDP, na koma APC - Dogara

Dalilin da yasa na bar PDP, na koma APC - Dogara

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya yi bayani a kan dalilin da yasa ya bar babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya koma jam'iyyar APC.

A ranar Juma'a, jaridar Premium Times ta ruwaito yadda Dogara ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan komawarsa jam'iyyar mai mulki.

A wasikar barin PDP da Dogara ya mika ga shugaban jam'iyyar na unguwar Bagoro, mai kwanan wata 24 ga Yulin 2020, ya ce rushewar shugabanci a jiharsa karkashin mulkin Gwamna Bala Mohammed yasa ya bar jam'iyyar.

Tsohon kakakin ya ce ba zai yi nasarar tambaya ba a kan al'amura ba tare da an zarge shi da rashin biyayya ba in har zai ci gaba da zama a PDP.

Dalilin da yasa na koma APC - Dogara
Dalilin da yasa na koma APC - Dogara Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Ya ce matukar zai yi watsi da dabi'ar fadin gaskiya ga shugabanni a jihar Bauchi, bayan wanda ya yi a zamanin mulkin Isa Yuguda da Mohammed Abubakar, zai zama mara akida a siyasar jihar.

Wannan bayanin na kunshe ne a wasikar da kakakin Dogara, Turaki Hassan, ya mika ga jaridar Premium Times.

An zabi Dogara a 2015 karkashin jam'iyyar APC. Ya koma jam'iyyar PDP tare da wasu magoya bayansa kafin zaben 2019.

Ya yi nasarar komawa majalisar a karkashin jam'iyyar PDP amma bai nemi kujerar kakakin ba saboda jam'iyyar APC ce ke da rinjaye a majalisar.

KU KARANTA KUMA: Dan majalisa daga Zamfara ya bayar da tallafi na miliyoyin naira ga al'umman mazabarsa (hotuna)

Bayan ganawarsa da Shugaban kasa a ranar Juma'a, shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Mala Buni, wanda ya halarci taron, ya ce Buhari ya yi farin ciki da wannan sauya shekar.

"Buhari ya yi maraba da shi. Ya ji matukar dadi da wannan ci gaban. Abinda yake so kenan. Muna gina jam'iyyar kuma matakan da muke dauka kenan wurin sake ginata," shugaban APC yace.

A baya mun ji cewa, hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya ce Yakubu Dogara, wanda ya dawo jam’iyyar Progressives Congress (APC) bai aikata kowani laifi ba.

A cewarsa, tsohon kakakin majalisar bai take doka ba a wannan hukunci da ya yanke.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel