Ba za mu iya janye sarautar Fani-Kayode ba - Shinkafi
Masarautar Shinkafi ta jihar Zamfara ta ce ba za ta iya janye sarautar da ta bai wa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ba, saboda sarautar ba a iya kwaceta.
Sarkin Shinkafi, Alhaji Muhammad Maikwashe a makon da ya gabata, ya bai wa Fani-Kayode sarautar Sardaunan Shinkafi.
Amma wasu daga cikin 'yan masarautar da 'yan siyasa sun yi zanga-zanga a kan hukuncin Sarkin.
Wasu masu sarauta biyar a masarautar Shinkafi sun tube rawaninsu a kan bada wannan sarautar ga Fani-Kayode.
Amma kuma, Wamban Shinkafi, Dr Sani Abdullahi Shinkafi a wata takarda da ya fitar a madadin masarautar Shinkafi a ranar Lahadi, ya ce sarkin yana da damar bai wa kowa sarautar da ya so kuma a lokacin da yaso.
Shinkafi ya yi kira ga jami'an tsaro da su gayyaci masu sarauta da suke zanga-zanga don tuhuma.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Zamfara ta raba raguna 5,000 da shanu 993
Ya ce, "suna buga kugen yaki tare da ruruta wutar rikicin addinni."
Shinkafi ya sanar da cewa masu sarauta biyar da suka yi murabus za a maye gurbinsu nan ba da dadewa ba kuma za a ja kunnen 'yan siyasa a kan saka siyasa da suke don kawo rikicin kabilanci da addinai a ciki.
"Sarautar da aka bai wa Fani-Kayode za ta sake gyara tsohuwar alakar da ke tsakanin mahaifinsa, Chief Remi Fani-Kayode da Alhaji Umaru Shinkafi. Sun yi aiki a wurin daya kuma ya mika dan sa ga Shinkafi amana.
"Kowa ya san marigayi Fani-Kayode yana daya daga cikin mutanen da suka nemi yancin kasar nan, dan kasa nagari ne kuma mataimakin shugaban yankin yamma. Mene ne matsalar bai wa dan sa sarauta.
"Femi Fani-Kayode ba shi kadai bane wanda ba Musulmi ba da ya taba samun sarauta a arewa.
"Akwai bukatar a sani cewa akwai 'yan kudu da yawa da aka bai wa sarauta kamar Olusegun Obasanjo wanda aka bai wa Yallaban Sokoto, Rocha's Okorocha da aka bai wa Danjekan Sokoto, Sanata Orji Uzo Kalu da aka bai wa Wakilin Anna da tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan da aka bai wa Garkuwan Manoman Zamfara.
"Babu kiyayya tsakanin Musulmi da Kirisfan arewa da kudu amma wasu suna son hura wutar kiyayyar siyasa ta kowanne hali.
"An zabesa ne saboda kokarin assasa hadin kai tsakanin 'yan Najeriya. Ya yi minista kuma kuma ya wakilci Najeriya gaba daya," masarautar tace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng