Gwamnatin jihar Zamfara ta raba raguna 5,000 da shanu 993

Gwamnatin jihar Zamfara ta raba raguna 5,000 da shanu 993

Gwamnatin jihar Zamfara ta fara raba raguna 5,667 da shanu 993 a matsayin tallafin babbar sallah ga jama'a daban-daban na fadin jihar.

Darakta janar na yada labarai da wayar da kai ga gwamnan jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Gusau a ranar Lahadi.

"Bisa ga al'ada, gwamnatin jihar karkashin shugabancin Gwamna Bello Matawalle yana cika alkawarinsa na bada kayan tallafi da rage radadi ga jama'ar jihar.

"Abinda muka yi kenan da karamar sallah inda muka bada tallafi ga jama'a daban-daban musamman marayu da kuma marasa karfi har 100,000. Sun samu kayan sawa, kayayyakin abinci da kuma kudi don shagalin sallah bayan kammala azumi.

Gwamnatin jihar Zamfara ta raba raguna 5,000 da shanu 993
Gwamnatin jihar Zamfara ta raba raguna 5,000 da shanu 993 Hoto: The Cable
Asali: UGC

"A wannan lokacin, iyalai da kungiyoyi daban-daban sun samu kyautatawa na kayan abinci da kayan sa wa don shagalin bikin babbar sallah da ke zuwa a ranar 31 ga watan Yuli," Idris yace.

KU KARANTA KUMA: Sunayen filayen jiragen sama 14 da ke hada-hada a Najeriya

Kamar yadda yace, an rarraba tallafin kayayyakin da wuri ta yadda za su amfana.

Kakakin gwamnan bai bayyana nawa aka yi amfani da shi wurin siyan raguna da shanun ba amma ya ce wadanda za su amfana sun kasance ma'aikatan gwamnati, kungiyoyi da sauransu.

A wani labari na daban, mun ji cewa asarautar Katsina ta kwaikwati jihar Kano inda ta yanke hukuncin soke dukkan shagulgulan sallar babba.

A shagalin duk babbar sallah, akwai fitaccen hawan nan da ake kira hawan bariki wanda sarki ne ziyartar gwamnan jihar tare da hawan daba mai kayatarwa.

Wannan na kunshe ne a wata wasika da masarautar ta tura ga sakataren gwamnatin jihar da kuma sa hannun sakataren masarautar Katsina, Mamman Ifo.

Kamar yadda wasikar ta ce, an soke shagulgulan sallar ne saboda hauhawar rashin tsaro da kuma annobar korona da ta addabi jihar.

Amma kuma, masarautar yayin da take taya daukacin Musulmi murna, ta yi kira garesu da su tsananta addu'a a kan Allah ya kawo zaman lafiya a jihar.

Babu takardar da ta bada tabbacin za a yi sallar idi ko ba za a yi ba a fadin jihar a yayin wannan rahoton.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel