Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Hausawa da wata kungiyar Yarabawa a Osogbo

Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Hausawa da wata kungiyar Yarabawa a Osogbo

Wata kungiyar 'yan daba karkashin jagorancin wani mutum da aka ambata da suna Ikeja sun yi artabu da 'yan kasuwar hausawa a ranar Asabar a jihar Osun.

An tattaro cewa da yawa daga cikinsu sun samu raunika amma ba a tabbatar da rasuwar ko mutum daya ba a yayin rubuta wannan rahoton.

An ga 'yan sanda dauke da makamai suna sintiri a yankin Sabo da ke Osogbo, babban birnin jihar don dawo da zaman lafiya.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ta sanar da The Punch cewa, "an tura 'yan sanda inda abun ya faru kuma a halin yanzu an shawo kan matsalar."

Wani mazaunin Sabo, Babatunde Ojo, wanda ke da alaka da rikici tsakanin dan achaba bahaushe da wani bakanike a ranar Juma'a, ya bada labarin yadda al'amarin ya faru.

Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa a Osogbo
Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa a Osogbo Hoto: Independent
Asali: UGC

Ojo ya ce dan achabar ya yi tukin ganganci inda ya kusa banke bakaniken wanda ke tafiya a kan titin Sabo-Oja.

KU KARANTA KUMA: Kano: Matashi ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwarsa za ta auri wani

Ya ce, "a yayin da bakaniken ya yi korafi a kan abinda dan achaban ya yi masa, sun yi musayar zafafan kalamai. Dan achaban ya isa teburin mai shayi inda ya dauko wuka wacce ya yi amfani da ita wurin harar bakaniken.

"A yayin martani, bakaniken ya bugi mai babur din da rodi kuma ya fadi. Ban san ko ya mutu ba. Sauran hausawan da ke wurin sun gaggauta isa tare da harar bakaniken wanda bayerabe ne.

"Wasu 'yan daba wadanda ke yankin sun isa wurin inda rikici ya hargitse."

A wani labari na daban, mun ji cewa an kashe mutane tara a wani hari da aka kai kan al’umman Zipkak da ke karamar hukumar Jama’a na jihar Kaduna.

Jama’a na daga cikin kananan hukumomin da gwamnatin Kaduna ta sanya dokar kulle na sa’o’i 24 saboda rashin tsaro amma duk da haka aka ci gaba da kai hare-hare.

An tattaro cewa ‘yan bindiga sun far ma kauyen, wanda ya ke kimanin rabin kilomita daga Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jama’a, da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Juma’a.

Gideon Mutum, wani mazaunin yankin, ya ce kimanin kwanaki uku da suka gabata, an yada jita-jitan cewa za a kawo hari amma ba a tsaurara matakan tsaro ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng