Watakila NARD za ta kuma shiga yaji a dalilin rashin alawus da kayan aiki a asibiti

Watakila NARD za ta kuma shiga yaji a dalilin rashin alawus da kayan aiki a asibiti

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa kungiyar NARD ta manyan likitocin Najeriya ta na barazanar cigaba da yajin aikin da ta dakatar kwanaki.

Kungiyar NARD ta likitocin fadin kasar nan za ta iya cigaba da yajin aikin da ta dakatar a ranar 17 ga watan Agusta muddin gwamnati ba ta biya mata bukatunta ba.

Wannan gargadi da NARD ta yi a ranar Asabar, 25 ga watan Yuli, 2020, ya zo ne bayan kungiyar ta kammala wani taron shugabanninta da ta shirya dazu a jihar Gombe.

Ta ce: “Kungiya ta yanke matakin tsawaita dakatar da yajin aiki da ta yi na tsawin makonni uku domin ba gwamnati damar sauraron korafinta.”

NARD ta ce: “Gazawa biyan wadannan bukatu zai bar kungiyar ba tare da wani zabi ba face komawa yajin aiki a ranar 17 ga watan Agusta, 2020.”

Wadanda su ka sa hannu a jawabin su ne: Shugaban kungiyar na kasa, sakatare, da sakataren yada labarai; Dr. Sokomba Aliyu, Dr.Bilqis Muhammad da Dr. Egbogu Stanley.

KU KARANTA: Abin da ya sa na bar NDDC - Kwankwaso

NARD za ta kuma shiga yaji a dalilin rashin alawus da kayan aiki a asibiti
Likitoci a Najeriya
Asali: Depositphotos

Wannan jawabi da shugabannin su ka fitar a madadin NARD ya bayyana cewa sharudan janye yajin sun hada tsige shugaban jami’ar UPTH, Farfesa Henry Ugboma.

An kuma bukaci gwamnati ta dawo da tsofaffin jami’an kungiyar ARD da aka dakatar daga aiki a UPTH. Ana zargin Ugboma da laifuffuka da su ka hada da sata da sabawa doka.

Sauran bukatun kungiyar sun hada da: “A samar da kudi domin sayen kayan bada kariya, ayi maza-maza a fitar da kudin horas da likitoci kamar yadda aka yi yarjejeniya.”

Jaridar ta ce NARD ta bukaci a biya duk wasu gibi da aka yi wa likitocin a albashinsu. Haka zalika kungiyar ta na bukatar a biya alawus din shiga hadari saboda halin annobar COVID-19.

A cewar kungiyar, lokaci ya yi da za a biya likitoci alawus dinsu, sannan kuma akwai bukatar horas da ma’aikatan asibitocin gwamnati jiha da ke kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng