Ana rade-radin Tofowomo ya kori Mukarrabai sakamakon rasa zaben fitar da gwani

Ana rade-radin Tofowomo ya kori Mukarrabai sakamakon rasa zaben fitar da gwani

Jaridar Vanguard ta samu rahoto cewa Nicholas Tofowomo ya nuna rashin jin dadinsa bayan ‘dan takararsa ya fadi zaben fitar da gwanin jam’iyyar PDP a Ondo.

Sanata Nicholas Tofowomo ya marawa Honarabul Banji Okunomo ne a zaben PDP na tsaida ‘dan takarar gwamnan jihar Ondo, a karshe ya sha kasa hannun Eyitayo Jegede.

‘Dan majalisar ya fusata ne da yadda tarin Hadimansa su ka gaza taimakawa Banji Okunomo samun nasara a zaben fitar da gwanin da aka yi a makon da ya gabata.

Rahoton ya ce Nicholas Tofowomo ya na da mukarrabai kimanin 92 da ke karkashinsa wadanda su ke karbar albashin N50, 000 zuwa N100, 000 duk wata.

Duk da kokarin da ‘dan siyasar ya ke yi, Agboolo ya zo na biyar ne a zaben bayan Eyitayo Jegede SAN da kuri’a 90.

Banji Okunomo tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo ya sauya-sheka daf da za a gudanar da zaben tsaida ‘dan takara a jam’iyyar hamayya ta PDP.

KU KARANTA: An yi rikici tsakanin Magoya bayan PDP da APC

Ana rade-radin Tofowomo ya kori Mukarrabai sakamakon rasa zaben fitar da gwani
Sanata Nicholas Tofowomo
Asali: UGC

Eyitayo Jegede ya tashi da kuri’a fiye da kuri’a 800 a PDP, wannan lamari ya ba har su hadiman Nicholas Tofowomo da mamaki.

Masu ba Sanatan shawara sun bayyanawa jaridar sallamarsu da aka yi a matsayin rashin adalci da zalunci.

Wani daga cikin wanda abin ya shafa ya tabbatar da cewa ya dauki mukarraban aiki ne a shekarar da ta gabata, ya ce an sallame su ne a ranar 24 ga watan Yuli.

Mista Akinrinlola Olumide, mai taimakawa Sanatan da kudancin jihar Ondo wajen harkokin yada labarai, ya yi karin haske game da dalilin sallamar masu bada shawarar.

“Ya kamata a sani cewa korar su bai da alaka da sakamakon zaben fitar da gwani saboda Sanatan bai da wani ‘dan takara a zaben.”

Akinrinlola Olumide ya kara da cewa Sanatan ya tsige wadannan mutane ne domin wadanda su ka yi masa aikin yakin neman zabe su na da yawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel