Dowowar Dogara babban cikas ne ga martabar jam’iyyar – Babban hadimin Buhari

Dowowar Dogara babban cikas ne ga martabar jam’iyyar – Babban hadimin Buhari

- Lauyan tsarin mulki, Itse Sagay, ya yi martani a kan dawowar Dogara jam’iyyar APC

- Dogara, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai, ya sauya sheka zuwa PDP a 2019

- Tsohon kakakin majalisar ya sake dawowa tsohuwar jam’iyyarsa a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuli

Tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa a kan yaki da cin hanci da rashawa (PACAC), Farfesa Itse Sagay, ya bayyana dawowar tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin babban cikas ga martabar jam’iyyar.

Daily Independent ta ruwaito cewa an yi wa Dogara jagoranci zuwa wajen Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuli.

Legit.ng ta tattaro cewa Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni, ya jagoranci Dogara zuwa fadar Shugaban kasa don ganawa da Buhari inda aka kammala dawowarsa jam’iyyar mai mulki.

Da yake martani ga ci gaban, Sagay ya ce a matsayin APC na jam’iyya mai ka’ida da bata bari Dogara ya dawo inuwarta ba.

Dowowar Dogara babban cikas ne ga martabar jam’iyyar – Babban hadimin Buhari
Dowowar Dogara babban cikas ne ga martabar jam’iyyar – Babban hadimin Buhari Hoto: The Interview Magazine
Asali: UGC

Ya ce: “A gani na, wannan babban cikas ne ga martabar APC. Ina ganin wannan nuni ga cewar bamu dauki akidoji da ka’idoji ba a siyasarmu. Saboda idan kana da wani akida, ba za ka dunga tsalle daga wannan jam’iyya zuwa wata ba.

“Don haka, yana sa ayi wa Najeriya da jam’iyyun siyasarmu kallon marasa wayau. Idan ba haka ba, babu wanda ya kori Dogara daga APC. Ya wayi gari ne wata rana sannan ya yanke shawarar bin abokinsa Saraki zuwa PDP. Menene dalilin da yasa bai tsaya a chan ba? Me yasa ya dawo APC? Don haka, a gareni babu banbanci tsakanin jam’iyyun biyu.

“Idan ba daya muke ba, kenan idan mutum ya ga wani abu mai kyau a PDP da ya sa shi komawa chan, mu bar shi ya ci gaba da kasancewa a chan ba wai mu yarda dashi ba kuma. Ya zama dole a dakatar da wannan hukunci na barin mutane na shiga da fita a jam’iyyu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel