Binciken Magu gagarumin nasara ne, in ji Malami
- Abubakar Malami ya sake tsokaci a kan binciken tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu
- Ana binciken Magu a kan zargin rashawa da ake masa
- Ministan shari'an ya bayyana binciken Magu a matsayin nasarar shugaban kasa Buhari
Atoni janar na tarayya, Abubakar Malami, ya ce binciken Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu da ake yi ya kara nuna nagartar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Malami ya fadi hakan a wani shirin NTA a daren ranar Juma’a, da yake mayar da martani ga tambayoyin mai gudanar da shirin, Cyril Stober.
AGF din ya bayyana cewa binciken dakataccen Shugaban na EFCC ya nuna cewa babu wanda ya fi karfin doka, Jaridar The Punch ta ruwaito.
Da yake amsa tambaya kan ko ana gudanar da binciken don wani rashin jituwa da ke tsakaninsu ne, ministan shari’an ya ce ba shine ke binciken EFCC din ba, cewa fadar shugaban kasa ce ta kafa kwamitin binciken.
Malami ya ce: “kafa kwamitin da fadar shugaban kasa ta yi domin binciken ayyukan hukumar yaki da rashawa ci gaba ne.
“Ya kasance abunda aka san wannan gwamnati a kai; na rashin tsoro ko yin alfarma idan har abu ya shafi bincike a kan zargin rashawa. Don haka, Ina ganin ci gaba ne wanda aka san gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kai cewa babu wani zargin rashawa da zai tafi ba tare da an bincike shi ba. Don haka ci gaba ne ba abun kunya ba.”
Fadar shugaban kasar ta dakatar da Magu da manyan jami’an EFCC kimanin 11 ciki harda sakataren hukumar, Ola Olukoyede.
KU KARANTA KUMA: Dogara bai karya kowani doka ba don ya bar PDP, in ji hadimin Buhari
Ana zargin hukumar EFCC karkashin Magu da rashin bayar da bayani daidai kan kudaden da aka kwato daga mahamdama.
Ana kuma zargin shugaban EFCC da siyan wasu kadarori a Dubai da ya kai naira miliyan 570.
An tsare Magu na kimanin kwanaki 10 kafin aka sake shi. Sai dai ya karyata zarge-zargen da ake masa.
Duk wani yunkuri na dakataccen shugaban na EFCC domin ya kare kanshi a gaban kwamitin ya ci tura.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng