Dogara bai karya kowani doka ba don ya bar PDP, in ji hadimin Buhari

Dogara bai karya kowani doka ba don ya bar PDP, in ji hadimin Buhari

- Ahmad ya yaba ma sauya shekar Yakubu Dogara

- A cewar hadimin shugaban kasar, dan majalisar bai take kowani doka ba

- Ku tuna cewa Dogara ya sauya sheka daga jam’iyyar APC kafin zaben 2019

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, wanda ya dawo jam’iyyar Progressives Congress (APC) bai aikata kowani laifi ba kamar yadda hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bayyana.

A cewarsa, tsohon kakakin majalisar bai take doka ba a wannan hukunci da ya yanke.

Ya wallafa a shafinsa na twitter cewa: "Wannan shine ainahin siyasa, ba a karya kowani doka ba a nan, Obaseki ya tafi kuma dogara ya dawo. Wannan shine tsarin wannan wasar, idan ka tafi, wani zai dawo ya cike gurbin. Kuma zai ci gaba a haka har zuwa karshen wasan. abu mafi ahla, kada ka damu kanka a kai. Ka kasance a tsaka-tsaki."

Ku tuna cewa Dogara ya bar APC zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da tsohon Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da wasu gwamnoni gabannin zaben 2019.

Dogara bai karya kowani doka ba don ya bar PDP, in ji hadimin Buhari
Dogara bai karya kowani doka ba don ya bar PDP, in ji hadimin Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gombe: An yanke wa tsohon shugaban karamar hukuma shekara 31 a gidan kaso

A baya dai Legit.ng ta rahoto cewa tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Yakubu Dogara ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ya koma APC.

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni ne ya tabbatar da hakan bayan ganawar da suka yi da Shugaba Buhari a yau Juma'a a Abuja.

Buni, yayin amsa tambayoyin manema labarai ya ce, "Bai kamata ƴan Najeriya su yi mamaki ba saboda dama tsohon Kakakin ɗan APC ne. Dalilin da yasa ya bar APC ta gushe."

An tambayi Buni ko dawowar Dogara APC na da alaƙa da zaɓen 2023, ya ce, "Eh, ba ma shirin zaɓen 2023 ba, muna saita jam'iyyar ne ta yadda ko bayan mu za ta cigaba da bunƙasa.

"Ba batun yanzu kawai ake ba ko wani ƙanƙanin lokaci, ba maganan zaɓe bane ko yaƙin neman zabe, magana ce ta gina jam'iyya."

Shugaban riƙon na APC da ya ke magana kan ƙoƙarin da suke na zawarcin tsaffin ƴan jam'iyyar ya ce, "Muna ganawa da tsaffin ƴan jam'iyyar mu musamman waɗanda ke da niyyar dawowa. Muna maraba da su. Muna tabbatar musu zamu yi musu adalci.

"Za mu yi wa dukkan mambobin mu adalci don hakan ne zai haifar da zaman lafiya, hakan zai sa jam'iyya ta ƙarfafa da kuma gina ta. Idan babu adalci, hakan ba zai yi su ba kuma muna da tabbacin zamu yi wa kowa adalci."

Buni ya ce ya ziyarci shugaban kasa ne kan batun ƙoƙarin da su ke yi na gina jam'iyya kuma "ya sanar da shi cigaban da ake samu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel