Ma'aikatar kwadago ga majalisar: Keyamo ne zai kula da daukar aiki 774,000

Ma'aikatar kwadago ga majalisar: Keyamo ne zai kula da daukar aiki 774,000

- Ma'aikatar kwadago ta ce lallai karamin ministanta, Festus Keyamo ne zai jagoranci daukar ma'aikatar 774,000

- Hakan martani ne ga bukatar majalisar tarayya na cewa a dakatar da ministan daga shugabantar daukar ayyukan

- Majalisar dattawan ta ce a maimakon ministan, a bai wa NDE damar jagorantar al'amarin

Ma'aikatar kwadago da aikin yi ta ce karamin ministanta, Festus Keyamo ne zai jagoranci daukar ma'aikata 774,000 a karkashin shirin ma'aikatar ta musamman.

Ma'aikatar ta sanar da hakan ne a martanin da tayi a kan bukatar majalisar tarayya na cewa a dakatar da ministan daga shugabantar daukar aikin.

Majalisar dattawan ta ce a maimakon ministan, a bai wa hukumar NDE damar jagorantar al'amarin.

Keyamo ya yi musayar kalamai da wasu 'yan majalisar a yayin da ya bayyana gaban kwamitin su don bayani a kan shirin.

Ma'aikatar kwadago ga majalisar: Keyamo ne zai kula da daukar aiki 774,000
Ma'aikatar kwadago ga majalisar: Keyamo ne zai kula da daukar aiki 774,000 Hoto: The Cable
Asali: UGC

'Yan majalisar sun zargi Keyamo da kanainaye shirin a maimakon mika shi ga NDE, amma ministan ya yi martani inda yace suna so ne a basu wasu gurabe na aikin.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni 8 a Najeriya da suka harbu da cutar korona

Daga bisani, majalisar dattawa ta dakatar da shirin kwata-kwata.

Idan za ku tuna, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Keyamo da ya ci gaba da shirin daukar aikin duk da matsayar 'yan majalisar.

A yayin zantawa da jaridar The Punch a ranar Laraba, Charles Akpan, mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar kwadagon, ya ce har yanzu Keyamo ne ke kan gaba wurin shirin.

Ya ce babu abinda aka canza tun bayan da Buhari ya bada damar farawa.

Akpan ya ce Keyamo ne zai ci gaba da jagorantar shirin wanda ake yi karkashin NDE.

"Shirin ayyukan na musamman na tare da NDE, amma ma'aikatar kwadago ke da alhakin kula da shi ta hannun ministan," yace.

"A don haka, duk abinda NDE tayi za ta mika rahoton ga karamin ministan, don haka babu abinda ya canza."

Keyamo ya jan kunnen Nasir Laden, darakta janar na hukumar NDE, a kan abinda zai iya fuskanta matukar ya take umarninsa a kan shirin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel