Saka bam a NNPC da NASS: Kotu ta yankewa mai laifi shekaru 2 a gidan yari

Saka bam a NNPC da NASS: Kotu ta yankewa mai laifi shekaru 2 a gidan yari

Kotu ta yankewa Godwin Adeoye mai shekaru 35 hukunci bayan da aka kama shi da laifin kokarin tada bam a majalisar dattawa da kuma kamfanin tace man fetur na Najeriya (NNPC).

Alkalin kotun majistare ta biyu da ke zama a Lokoja, jihar Kogi, a ranar Laraba, ya yankewa Adeoye hukuncin shekaru biyu a gidan gyaran hali a kan laifinsa.

Adeoye dan asalin karamar hukumar Okene ne wanda ke zama a Obehira Ihema da ke karamar hukumar Okehi ta jihar.

Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya ne suka dauke shi a ranar 13 ga watan Mayun 2020. Daga bisani an mika shi ga ban kotu tare da aka zargesa da barazanar saka wa kadarorin gwamnati bam.

Alkalin kotun majistaren, A. S Ibrahim, ya ce wanda ake zargin ya fashe da kuka tare da neman rangwame bayan ya gane irin laifin da yayi yunkurin aikatawa. An yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan gyaran hali.

Amma kuma, lauyan DSS, O. Yahaya ya sanar da Daily Trust cewa ana sake duba shari'ar.

"Muna nazari tare da sake duba shari'ar tare da tunanin za mu daukaka kara ko a'a," yace.

Saka bam a NNPC da NASS: Kotu ta yankewa mai laifi shekaru 2 a gidan yari
Saka bam a NNPC da NASS: Kotu ta yankewa mai laifi shekaru 2 a gidan yari. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Boko Haram ta saki bidiyon kisan gilla da suka yi wa ma'aikatan SEMA da mai gadi

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojin saman Rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaza sansanin 'yan bindiga a samamen da ta kai ta jiragen yaki a dajin Kagara na jihar Zamfara.

Kamar yadda Shugaban fannin yada labarai na rundunar, John Enenche ya sanar a ranar Laraba a Abuja, dakarun sun kai samamen ne a ranar 20 ga watan Yulin 2020.

Enenche ya ce sun kai samamen ne bayan rahotannin sirri da suka samu na 'yan bindigar da ke dajin tare da dabbobin da suka sace a wani sassa na dajin.

Ya ce an tabbatar da rahotannin sirrin bayan leken asirin da aka yi ta jiragen yaki. Hakan ne yasa aka ragargaza maboyar da ruwan bama-bamai.

Kamar yadda yace, jiragen rundunar sojin saman sun isa wurin inda suka dinga ruwan bama-bamai da ya kai ga kisan wasu daga cikin 'yan bindigar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel