Wata sabuwa: An yi musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da dan majalisa

Wata sabuwa: An yi musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da dan majalisa

- Wani abun mamaki mai kama da wasan kwaikwayo ya auku a majalisar wakilai a ranar Talata, 21 ga watan Yuli

- Ministan kwadago ya bayyana a gaban kwamitin majalisar a kan harkallar da ke tattare da hukumar NSITF

- Amma kuma Ngige da James Faleke, dan majalisa mai wakiltar Legas, sun yi musayar miyagun kalamai

Abinda ya kamata ya zama tamkar tattaunawa a kan harkallar hukumar kula da inshora ta kasa (NSITF), ya koma wani fada mai alaka da siyasa a majalisar dokokin tarayya a ranar Talata, 21 ga watan Yuli.

Wani kwamitin majalisar wakilai ya gayyaci ministan kwadago, Chris Ngige a kan abinda ya shafi hukumar NSITF.

Amma kuma yayin sauraron lamarin, wani karamar wasan kwaikwayo ya auku tsakanin ministan da dan majalisa James Faleke, mai wakiltar Ikeja.

Gidan talabijin na Channels TV ya nadi bidiyon wanda ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani.

"Kai tamkar karamin kanina kake. Sai dai kuma idan an ce Faleke ya kai shekaru 60, toh wannan ban sani ba," Ngige yace yayin da ya fara sanar da dan majalisar cewa ya girmeshi.

A take Faleke ya yi martani, "Shekaru na sitti da doriya..."

"Kenan ka kusa da shekaruna, akalla na girme ka da shekaru bakwai. Shekaruna daya da ubangidanka na jihar Legas, Asiwaju," ministan ya sake martani, yana mai misali da babban jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu.

"Kuma na yi gwamna a lokaci daya da shi. Ya yi Sanata kuma nima nayi. Na yi minista sau biyu, shi bai yi ba," ya kara da cewa.

Faleke ya mayar masa da cewa, "amma Tinubu ya ci dukkanin zabukan da ya tsaya." Yana habaici ne a kan rikicin zaben jihar Anambra na Ngige.

Wata sabuwa: An yi musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da dan majalisa
Wata sabuwa: An yi musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da dan majalisa
Asali: UGC

Ngige ya yi martani da cewa, "babu damuwa a kan hakan. Kamar yadda kaima ka ci zabenka na jihar Kogi kuma kaine mataimakin gwamna da gwamnan jihar a yanzu."

Ngige na habaici ne a kan ta leko ta koma da Faleke ya gani a jihar Kogi yayin da Abubakar Audu ya ci zabe kuma ya rasu.

Ya so karbar tikitin neman kujerar gwamnan jihar amma aka hana shi.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta amince da nadin jakadu 39

A lokacin da Faleke ya bukaci ministan da ya amsa tambayoyinsa, ya ce: "ina amsawa ne abokina. Idan ka yi min shagube daya, sai nayi maka sau goma. Nima dan Legas ne.

"Kalli wannan yaron yankin Mushi, yana magana da dan VI. A asibitin Victoria na zauna. Kalli wannan yaron Mushin da ya fito daga Kogi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel