Akwai yiwuwar sai Buhari da Shugabannin ECOWAS sun shiga Mali – Goodluck Jonathan

Akwai yiwuwar sai Buhari da Shugabannin ECOWAS sun shiga Mali – Goodluck Jonathan

Jakadan musamman da kungiyar kasashen yammacin Afrika ta aika zuwa Mali, Dr. Goodluck Jonathan ya ce watakila sai manyan ECOWAS sun kai ziyara zuwa kasar.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nuna akwai yiwuwar Muhammadu Buhari da wasu shugabannin kasashen yankin Nahiyar su ziyarci kasar Mali da ake fama da rikici.

Goodluck Jonathan wanda ya jagoranci tawagar sulhu da ECOWAS ta tura zuwa kasar Mali ya bayyana haka ne lokacin da ya zanta da manema labarai a fadar shugaban Najeriya a Abuja.

Idan ba ku manta ba Goodluck Jonathan ya na babban birnin tarayya a jiya ranar Talata.

A matsayinsa na Jakadan zaman lafiya zuwa kasar Yammacin Afrikar, Jonathan ya yi wa Buhari bayanin halin da ake ciki a Mali inda ake yi wa shugaba Ibrahim Boubacar Keita zanga-zanga

Shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita ya shafe shekaru biyu cikin shekaru biyar da ya ke da su a ofis, amma an samu ‘yan tawaye da su ka huro masa wuta a kan ya yi murabus.

KU KARANTA: Bidiyon Jonathan ya na yabon Shugaba Buhari

Akwai yiwuwar sai Shugabannin ECOWAS su shiga kasar Mali – Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan Hoto: Facebook
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ce ‘yan wata kungiya da ake kira M5 ne su ka taso shugaban na Mali a gaba, musamman bayan kotu ta ruguza sakamakon zaben majalisun tarayya da aka yi.

Barkewar rikicin siyasar da ya yi sanadiyyar kashe mutane ne ya jawo ECOWAS ta tada dakaru domin su kawo zaman lafiya. Ana sa ran a ga karshen wannan rigima ba da dadewa ba.

“Mun isa Mali a ranar Laraba (makon jiya). Mun fara wannan aiki a daren ranar. Wanda mu ka fara ganawa da shi shi ne shugaban kasar, sai firayim minista, sai wasu kungiyoyi.” Inji Jonathan.

“Mun bar kasar ranar Lahadi da yamma, babu shakka shugaban kasarmu (Buhari) wanda jagora ne a kungiyar ECOWAS ne ya bada jirgin da ya dauke mu kuma ya maido mu.”

Jonathan ya cigaba da cewa: “Watakila sai shugaban kasar ya koma Mali tare da wasu. Saboda haka ya na da kyau idan ka je ka yi irin wannan aiki ka dawo, ka sanar da shugaban kasa.”

Idan har shugaban Najeriyar ya yi wannan tafiya zuwa Mali, za ta zamo ta farko da ya yi tun watan Fubrairu. A shekarar nan, sau biyu Buhari ya bar gida, watakila saboda annobar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng