Kudin Mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos ya karu da $13bn a ranar Litinin

Kudin Mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos ya karu da $13bn a ranar Litinin

- A rana daya arzikin Jeff Bezos ya karu da kimanin $13bn a makon nan

- Abin da fitaccen Attajirin ya mallaka ya na neman kai Dala biliyan 200

- Bezos mai shekaru 56 a Duniya shi ne mai kamfanin cefane na Amazon

Shugaban babban kamfanin nan na Amazon, Jeff Bezos ya motsa gaba a sahun attajiran Duniya bayan dukiyarsa ta karu da fam Dala biliyan 13.

Alkaluman Bloomberg Billionaires Index na BBI sun bayyana cewa Jeff Bezos mai shekara 56 ya samu wadannan makudan kudi ne dare guda a farkon makon nan.

Tun da aka kafa BBI shekaru takwas da su ka wuce, ba a taba samun lokacin da wani attajiri ya lula sama a rana daya kamar yadda Bezos ya motsa a ranar Litinin ba.

Rahoton ya bayyana cewa arzikin Bezos ya karu ne a sakamakon kumburar da hannun jarin kamfaninsa ya yi da 7.9%, darajar da Amazon bai yi ba tun karshen 2018.

Masu nazarin tattalin arziki sun ce Amazon na kara samun karbuwa ne a sanadiyyar yadda jama’a su ke kara yi da kafafen hada-hada na zamani.

KU KARANTA: Bezos zai rabu da mai dakinsa

Bloomberg ta ce jimillar arzikin Mista Bezos ta karu da fam Dala biliyan $74.4 a shekarar nan ta 2020. Bill Gates da ke biye a baya ya na da fam biliyan $113.

Abin da wannan ya ke nufi shi ne Bezos ya ba Dala biliyan 189 baya a halin yanzu. A kudin gida, kudin Attajirin sun haura Naira Tiriliyan 77, 256, 000, 000.

Da wannan makukun arziki, Bezos ya fi kamfanin Exxon, Mobil Corp., Nike Inc da McDonald’s Corp duk a dunkule kudi.

Wannan kudi da Bezos ya samu a rana guda ya neman ribanya dukiyar Aliko Dangote biyu, wanda shi ne mai kudin kaf Nahiyar Afrika da kimanin Dala biliyan 7 a asusunsa.

Idan ba za ku manta ba, a farkon shekarar nan Jeff Bezos ya rasa kusan Dala biliyan 10 a rana guda. Bayan nan Attajirin ya murmure, arzikinsa kuma ya fi na da.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel