Dangantakata da Buhari lafiya lau ta ke tafiya – Goodluck Jonathan ya yabi Shugaban kasa

Dangantakata da Buhari lafiya lau ta ke tafiya – Goodluck Jonathan ya yabi Shugaban kasa

Tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya ce babu wata matsala tsakaninsa da magajinsa, shugaban kasa mai-ci Muhammadu Buhari.

Duk da cewa Muhammadu Buhari ne ya tika Goodluck Jonathan da kasa a zaben 2015, sanadiyyar barinsa kan mulki, ya ce alakarsa da shugaban kasar lafiya kalau ta ke.

Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuli, 2020, lokacin da ya ke amsa tambayoyi a gaban ‘yan jarida a fadar shugaban kasa.

Idan ba ku manta ba, tsohon shugaban kasar ya ziyarci Muhammadu Buhari, inda ya yi masa bayani game da yunkurin da ECOWAS ta ke yi game da rikicin kasar Mali.

Jonathan ya kai wa shugaban kasar ziyara ne tare da shugaban kungiyar ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou jiya da rana.

Da aka tambayesa game da dangantakarsa da Buhari, Jonathan ya bada amsa cewa: “Ku na gani na ina zuwa nan, kuma mu na tattaunawa salin-alin.”

KU KARANTA: Jonathan da Buhari sun hadu a Abuja

Dangantakata da Buhari lafiya lau ta ke tafiya – Goodluck Jonathan ya yabi Shugaban kasa
Shugaban kasa Buhari da Jonathan Hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: Twitter

“Saboda haka alakata da shi lafiya lau.” Inji tsohon shugaban na Najeriya.

Tsohon shugaban kasar bai tsaya a nan ba, ya yabi shugaba Buhari a kan karasa aikin jirgin kasan Itakpe-Warri da ya yi, ya kuma sa sunan Goodluck Jonathan.

“Bari in yi amfani da wannan dama in jinjinawa shugaban kasa a fili. Na tura masa wasikar godiya na abin a yaba da ya yi.” Inji Jonathan.

“Kammala aikin jirgin kasar abu ne me kyau. Ya nuna cewa shugaban kasa ya na karasa manyan ayyukan da gwamnatocin baya su ka fara.”

“Haka ya kamata a rika tafiya. Na aika masa wasika. Na yaba masa da fatar baki kuma, tun da kuma kun tambaye ni, bari in yi wannan a bainar jama’a.”

Goodluck Jonathan ya kare da cewa: “Na godewa shugaban kasa, ministan sufuri da duk wadanda su ka tabbatar wajen ganin an yi wannan.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel