Suna da jiha: Rundunar 'yan sanda ta nada sabbin kwamishinoni a jihohi 5

Suna da jiha: Rundunar 'yan sanda ta nada sabbin kwamishinoni a jihohi 5

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cewa babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya amince da nadin sabbin kwamishinoni (CP) a jihohi biyar.

Hakan na kunshe ne a cikin wani takaitaccen sako da rundunar 'yan sandan ta wallafa a shafinta na sada zumumta; watau Tuwita.

Sabbin kwamishinonin da jihohin da aka turasu sune kamar haka;

Ekiti State – CP Mobayo Babatunde, psc

Ogun State – CP Edward Awolowo Ajogun

Cross River State– CP Abdulkadir Jimoh, fsi

Bayelsa State – CP Okoli C. Michael, fsi

Sanarwar ta kara da cewa sabbin kwamishinonin za su fara aiki nan take.

Wannan shine karo na uku da rundunar 'yan sanda ta nada sabon kwamishina a jihar Delta, kamar yadda wasu masu bibiyar al'amuran jihar suka bayyana.

A wani labarin da ya shafi nadin mukamai, Legit.ng ta wallafa cewa wani lauya a jihar Legas, Lawarence Nnoli, ya shigar da karar neman babbar kotun tarayya da ke Lagas ta tilasta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kara yawan alkalan kotun koli.

Kasancewar wasu alkalan kotun koli sun yi ritaya kuma har yanzu ba a maye gurbinsu ba, adadin yawan alkalan kotun koli a Najeriya ya ragu zuwa 12 daga 21 da kundin mulki ya ambata.

Suna da jiha: Rundunar 'yan sanda ta nada sabbin kwamishinoni a jihohi 5
IGP Muhammad Adamu
Asali: Facebook

A cikin takardar karar da ya shigar a gaban kotun, Nnoli ya bayyana cewa rashin nada sauran alkalan "babbar saba doka ne, saboda ya sabawa sashe na 231(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999."

Da ya ke gabatar da hujjojinsa, Nnoli ya bayyana cewa tun watan Oktoba na shekarar 2019 hukumar kula da bangaren sharia (NJC) ta mika sunayen alkalan kotun koli hudu domin a daga darajarsu zuwa alkalan kotun koli.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa Jonathan ya ziyarci Buhari a Villa

Nnoli ya yi zargin cewa shugaba Buhari ya yi burus da bukatar NJC saboda har yanzu bai tura sunayen alkalan zuwa majalisar dattijai domin tabbatar dasu ba bayan kusan shekara guda.

Alkalan da NJC ta aika sunayensu sune kamar haka; Adamu Jauro, Emmanuel Agim, C. Oseji, da Helen Ogunwumiju.

Lauyan ya roki kotun ta bayar da wani umarni da zai tilasta shuagaba Buhari yin aikinsa.

Duk da kotun daukaka kara ta mika takardar karar mai lamba FHC/C/CS/897 zuwa kotun da Mohammed Liman ke jagoranta, har yanzu ba a saka ranar fara sauraron karar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel