FG ta daga ranar bude tashi da saukar jiragen sama zuwa ketare, ta saka sabuwar rana

FG ta daga ranar bude tashi da saukar jiragen sama zuwa ketare, ta saka sabuwar rana

- Gwamnatin tarayya ta dage lokacin fara tashi da saukar jiragenta zuwa kasashen ketare

- Jiragen za su fara zuwa ketare ne a watan Oktoba sabanin watan Agusta da ta bayyana a baya

- Hakan na cikin kokarin da take yi na dakile cutar coronavirus

Gwamnatin tarayya ta tsawaita lokacin fara tashi da saukar jiragenta zuwa kasashen ketare har zuwa watan Oktoban 2020.

Hukumar kula da sufirin jiragen sama mai zaman kanta ta Najeriya (NCAA) ta sanar da masu ruwa da tsaki cewa an fasa bude tashi da saukar jiragen saman zuwa kasashen ketare a ranar 19 ga watan Augusta.

Gwamnatin tarayya ta dakatar da tashi da saukar jiragen sama zuwa kasashen ketare a watan Maris bayan barkewar annobar korona amma ta bude tashi da saukar jiragen a cikin gida.

FG ta daga ranar bude tashi da saukar jiragen sama zuwa ketare, ta saka sabuwar rana
FG ta daga ranar bude tashi da saukar jiragen sama zuwa ketare, ta saka sabuwar rana Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Amma kuma kamfanoni da masu ruwa da tsaki sun ci gaba da matsanta wa gwamnati a kan ta dage dokar hana sauka da tashin jiragen saman zuwa kasashen ketare.

"Gwamnatin tarayya ta tsawaita lokacin bude filayen sauka da tashin jirage zuwa kasashen ketare.

"Amma kuma, NCAA ta ce za a iya mika bukata ta musamman a kan hakan kuma ta yuwu a amince. Za a mika wannan bukatar ga ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika." Kyaftin Musa Nuhu ya ce.

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin jihar Adamawa ta musanta zargin da hukumar FAAN ta yi wa gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri.

Hukmar FAAN ta zargesa da kin kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar korona a filin jirgin sama na Fatakwal a ranar Talata da ta gabata.

Darakta janar na yada labaran Fintiri, Solomon Kumangar, ya ce zargin da FAAN tayi mishi babu gaskiya a ciki saboda ba hakan bane ya faru a filin jirgin saman domin kuwa ya kiyaye dukkan dokokin da ake bukatar ya kiyaye.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Mutum 8 sun rasa rayukansu a sabon rikicin Zangon Kataf

Hadimin gwamnan ya ce Fintiri ya je Fatakwal ne don halartar taron a kan zaben jihar Edo tare da sauran gwamnonin PDP a wurin Gwamna Nyesom Wike.

Hadimin gwamnan ya ce Fintiri ya je Fatakwal ne don halartar taron a kan zaben jihar Edo tare da sauran gwamnonin PDP a wurin Gwamna Nyesom Wike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng