Sauran ƙiris a buɗe makarantun Islamiya a Kano - Gwani Yahuza

Sauran ƙiris a buɗe makarantun Islamiya a Kano - Gwani Yahuza

Mun samu rahoton cewa, ana daf da buɗe makarantun Islamiya a jihar Kano kamar yadda Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito.

Hukumar makarantun Islamiya ta jihar ta bukaci malamai iyaye da kuma ɗaliban makarantu da su ci gaba da daukan dangana a yayin da saura ƙiris a buɗe makarantun baki ɗaya.

Hukumar ta sanar da cewa nan ba daɗewa za a buɗe makarantu a yayin da gwamnatin jihar ta ke ci gaba da tattaunawa hukumomin lafiya bisa la'akari da annobar korona.

Shugaban hukumar, Sheikh Gwani Yahuza Gwani 'Dan Zarga, shi ne ya fayyace hakan a wata hira da ya yi da manema labarai.

Gwani Yahuza ya bayyana damuwar da gwamnatin jihar ta yi dangane da yadda ɗalibai ke ci gaba da zaman dirshan a gidan babu karatun Arabi bare na Boko sakamakon annobar korona.

Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Hakkin mallakar hoto; Fadar Gwamnatin Kano
Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje Hakkin mallakar hoto; Fadar Gwamnatin Kano
Asali: Twitter

Malamin sha kundum a ilimin Al-Qur'ani, ya ce tabbas annoba gaskiya ce kuma addinin Islama ya koyar daukan duk wasu matakan kariya yayin da ta bulla a cikin al'umma.

Ana iya tuna cewa tun a watan Maris ne gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe kafatanin makarantun kasar manya da kanana a matsayin matakin dakile yaduwar cutar korona wadda ta bulla karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ce Najeriya zata fuskanci wata babbar annoba ma damar ta kasa amfani da yanayin da annobar korona wajen bunkasa fannin kiwon lafiya.

KARANTA KUMA: Mudassir & Brothers ya dauki matasa 400 aiki a Kano

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Mr Boss Mustapha ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da hukumar kwararru (BoE) na shirin bincike da bunkasa kiwon lafiya (HSRDIS) a Abuja.

A cewar sa: "Idan har muka tsallake wannan yanayin, to lallai zamu fuskanci wata annobar kuma ba zamu iya tsinana komai ba.

"Idan da ace mun bunkasa fannin kiwon lafiya a lokacin annobar Ebola, da bamu sha wahalar da muka sha a yanzu ba, tunda cibiyoyin gwajin COVID-19 biyu kadai garemu."

Ya kara da cewa: "Idan da zaka zagaya kasar nan, zaka samu sama da cibiyoyin kiwon lafiya 10,000, amma kalilan ne ke da kayan aiki, wasu ma ba a amfani da su."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel