Dalilin da yasa Jonathan ya ziyarci Buhari a Villa

Dalilin da yasa Jonathan ya ziyarci Buhari a Villa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai tuntubi sauran shugabannin kasashen nahiyar Afrika a kan yadda za a samu zaman lafiya mai dorewa a kasar Mali mai fama da rigingimu daban - daban.

Buhari ya bayyana hakan ne bayan karbar rahoto daga wurin wakilin zaman lafiya na musamman da aka tura kasar Mali, tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan.

A cewar wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja, ya ce Jonathan ya samu rakiyar shugaban kungiyar ECOWAS, Mista Jean-Claude Kassi Brou.

"Za mu tattauna da shugaban kasar Nijar, wanda shine ciyaman na ECOWAS, domin ya gabatar da mana jawabi, daga nan kuma za mu san menene mafita," a cewar shugaba Buhari.

Buhari ya mika godiyarsa ga Jonathan a kan yadda ya bayar da lokacina wajen zuwa kasar Mali a matsayin wakili na musamman domin ya gano halin da take ciki dangane da batun tsaro.

Zanga - zangar neman shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita, ya sauka daga kan mulkinsa duk da yana da sauran shekaru uku a cikin biyar na zangon mulkinsa na biyu, ta rikide zuwa rikici

Dalilin da yasa Jonathan ya ziyarci Buhari a Villa
Dalilin da yasa Jonathan ya ziyarci Buhari a Villa
Asali: UGC

Wata kungiyar 'yan tawaye mai suna 'M5' ta bukaci a rushe kotunan kasar Mali da kundin tsarin mulki ya kafasu, sannan shugaba Keita ya yi murabus matukar ana bukatar samun lafiya a kasar.

DUBA WANNAN: Binciken badakala: Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori, ya fadi 'warwas' a gaban kwamiti

Rikici ya barke bayan kotunan kasar Mali sun kwace kujerun mambobin majalisa 31 tare da mikasu zuwa hannun wasu 'yan takara da aka bayyana sun fadi bayan kada kuri'a.

Kungiyar 'M5' ta yi zargin cewa kotunan sun aikata hakan ne bisa umarnin shugaba Keita.

Kungiyar ECOWAS ta yanke shawarar shiga rikicin kasar Mali bayan al'amura sun kara dagulewa a 'yan kwanakin baya bayan nan sakamakon kashe wasu masu zanga-zanga da jami'an tsaro su ka yi a ran 10 ga watan Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng