Jami'an EFCC 12 sun samu wasikar dakatarwa daga aiki
- An mika wa jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa su 12 wasikar sallama daga aiki
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin bincike na fadar shugaban kasa karkashin jagorancin Isa Ayo Salami ke ci gaba da tuhuwar wasu jami'an hukumar
- Kamar yadda aka gano, jami'an 12 sun samu wasikar dakatarwarsu a jiya Litinin, kuma zai kasance har illa MashaAllah
A kalla jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) su 12 aka dakatar a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, har illa MashaAllahu.
Ana ci gaba da tuhumar wasu jami'an hukumar a gaban kwamitin bincike na fadar shugaban kasa wanda ke samun shugabancin Mai shari'a Isa Ayo Salami.
Sai da aka tura motar daya daga cikin jami'an da aka tuhuma a gaban dakin taron da aka tuhumesa a fadar shugaban kasa kafin ya tashi.
Kamar yadda aka gano, jami'an 12 sun samu wasikar dakatarwarsu a jiya Litinin, jaridar The Nation ta ruwaito.
Wata majiya mai karfi ta ce: "Bayan adana su da aka yi na tsawon mako daya, sun samu wasikar dakatarwarsu a jiya.
"An sanar da cewa dakatarwar zai kasance har sai illa MashaAllahu. Mun dauki hakan a matsayin kaddara. Amma da yawa kuma daga cikinmu ba a basu wasikar tuhuma ba a kan aikinmu.
"Ba mu gurfana a gaban kwamiti ba. Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shiga wannan al'amari."
KU KARANTA KUMA: NDDC: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana wadanda aka bai wa kwangila
Wasu daga cikin jami'an da suka bayyana gaban kwamitin sun amsa tambayoyi daban-daban.
Daya daga cikin jami'an ya ce: "A gaskiya ba wasa bane tuhumar da aka yi mana amma mun iya yin wasu bayanai game da aikinmu.
"Daya daga cikin 'yan kwamitin ya ce bautawa kasa tare da biyayya ne makasudin zamansu a ofishinsu ba wai son rai ba."
A wani labarin, lauyan dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, Wahab Shittu, ya ce wanda yake karewa na tsammanin abun mamaki amma na alkhairi daga kwamitin fadar shugaban kasar a kan zargin da ake masa.
Shittu ya sanar da hakan ne a ranar Litinin a wani martani da yayi a kan maganar mataimaki na musamman ga shugaban kasa a fannin yada labarai, Garba Shehu.
Shehu dai ya yi wata hira ne da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, kan lamarin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng