Abin da ya sa David Umahi ya sallami Hadimai 1, 000 daga Gwamnatinsa

Abin da ya sa David Umahi ya sallami Hadimai 1, 000 daga Gwamnatinsa

- Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya salami Hadimansa fiye da 1, 000

- Mukarraban gwamnan da su ka rasa aiki sun kasance masu bada shawara

- Wannan mataki da gwamnan ya dauka zai fara aiki a cikin watan Agusta

Mai girma gwamnan jihar Ebonyi, Mista David Umahi, ya tsige sama da hadimai 1, 000 da ke aiki a kwamitocin kananan hukumomi da cibiyoyin cigaba a jihar.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta rahoto cewa gwamnan ya bada wannan sanarwa ne a jiya ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, 2020.

Sanarwar ta zo ne a lokacin da gwamna Dave Umahi ya nada wasu sababbin hadimai da kantomomi da za su rike kananan hukumomi na rikon kwarya.

NAN ta ce rukunin mukarraban da aka sallama daga aiki a jihar Ebonyi sun hada da masu taimakawa da wasu manyan masu ba gwamnan shawara.

KU KARANTA: COVID-19 ta harbi mutane 552 a ranar Litinin

Abin da ya sa David Umahi ya sallami Hadimai 1, 000 daga Gwamnatinsa
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi
Asali: Facebook

A cewar David Umahi, hadiman sun rasa kujerunsu ne saboda rashin yin aikin da ya dace. Wannan sallama da aka yi za ta fara aiki ne daga ranar Asabar, 1 ga watan Agusta.

“Mu na da sama da hadimai 1, 000 irin ku, da fiye da mukarrabai 350 a ofishohin kwamitoci da cibiyoyin cigaba a jihar, yayin da ni da mataimakina mu ke cikin wani hali a lamarin annobar COVID-19.”

Umahi ya cigaba da bayani, ya na cewa: “Ban san inda za ku samu mukami ace kawai ku na kwance ku na jiran kudi su shigo cikin asusunku a banki ba.”

Mai girma gwamnan ya fadawa hadiman da aka sallama cewa za su iya sake neman wannan aiki da su ka rasa, muddin sun samu takarda daga ma’aikata.

A ranar 4 ga watan Yuli ne mai magana da yawun gwamna Dave Umahi ya sanar da cewa gwamnan da wasu hadimansa sun kamu da kwayar cutar Coronavirus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel