Akeredolu ya yi nasara, ya samu tikitin takara a APC jihar Ondo

Akeredolu ya yi nasara, ya samu tikitin takara a APC jihar Ondo

- Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya yi nasarar samun tikitin takarar gwamnan jihar na APC

- Za a gudanar da zaben gwamnan Ondo a ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa

- Akeredolu ya kwashe kuri'u mafi rinjaye a zaben fidda gwani da aka yi a Dome a Akure, babban birnin jihar

Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, ya samu cafke tikitin takarar gwamnan jihar Ondo karkashin jam'iyyar APC wanda za a yi a ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa.

Gwamnan ya kwashe kuri'u mafi rinjaye a zaben fidda gwani da aka yi a Dome a Akure, babban birnin jihar.

A yayin sanarwa a kan yadda al'amarin ya faru, Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi kuma shugaban kwamitin zaben fidda gwanin jam'iyyar, ya ce Akeredolu ya samu kuri'a 2,458 yayin da Olusola Oke ya samu kuri'u 262 sai kuma Isaacs Kekemeke da ya samu kuri'u 19.

Akeredolu ya yi nasara, ya samu tikitin takara a APC jihar Ondo
Akeredolu ya yi nasara, ya samu tikitin takara a APC jihar Ondo Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Sama da wakilai 3,127 ne suka yi zaben fidda gwanin.

Hudu daga cikin 'yan takara 12 da suka nuna bukatarsu ta kujerar, sun janye saboda Akeredolu.

KU KAARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sallami Shugaban NDDC daga asibiti

'Yan takarar sune Ife Oyedele, Abraham Olusegun, Jimi Odimayo da Nathaniel Adojutelegan.

A yayin da ake shirin zaben, wasu daga cikin 'yan takarar sun nemi a yi zaben fidda gwani na kato bayan kato amma Bello ya ce ba za su iya fada wa jam'iyyar abunda za ta yi ba tunda ta yanke hukunci kan amfani da wakilai

Sauran 'yan takarar da suka shiga zaben sun hada da Awodeyi Akinsehinwa, Bukola Adetula, Sola Iji, Jumoke Anifowoshe da Olayide Adelami.

A wani labari na daban, Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya ba magoya bayan jam’iyyar tabbacin nasara a zaben gwamnan Edo mai zuwa.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a Edo a karshen mako, ya nuna karfin gwiwar cewa jam'iyyar APC za ta yi nasara a zaben wanda za a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.

Da yake hannunka mai sanda ga Godwin Obaseki, gwamnan jihar mai ci na jam'iyyar PDP, Oshiomhole ya ce ya yi farin ciki da cewar “Allah ya fitar da maciji.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng