Funtua: Sanata ya yi magana da shi daf da zai mutu, Saraki ya yi wa Buhari ta’aziyya
Sanata Ben Murray-Bruce, tsohon Sanatan Najeriya, ya bayyana yadda ya yi magana a wayar salula da Malam Ismail Isa Funtua a daren da zai cika.
Tsohon sanatan Bayelsa, ya ke cewa ya yi waya da Ismaila Isa Funtua a ranar Litinin, har dattijon ya yi alkawarin kiransa a waya yau, sai kuma kawai ya ji labarin rasuwarsa.
Ben Murray-Bruce ya rubuta: “Na ji takaicin mutuwar ‘danuwana kuma babban abokin aiki, Mallam Isa Funtua. Na yi magana da shi sa’o’i uku rak kafin a ji labarin mutuwarsa, har ya yi mani alkawarin zai kira ni gobe.”
Sanata Murray-Bruce ya kara da cewa: “Ina addu’a Ubangiji ya ba iyallinsa da masoyansa hakuri, kuma Ubangiji ya sa ya huta.”
Bisa dukkan alamu, Ben Murray Bruce mai shekaru 64 a Duniya ya na cikin aminan marigayin kuma wanda su ka san juna a harkar aikin jarida da yada labarai.
Shekara guda kenan da ‘dan siyasar ya rasa mai dakinsa bayan sun shafe shekaru 41 su na zaman aure.
KU KARANTA: Shugaban kasa ya yi jawabi bayan mutuwar Ismail Funtua
Shi ma tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi magana bayan ya samun labarin rasuwar wannan Bawan Allah.
Saraki ya rubuta: “InnalilLahi Wa Inna Ilaehi Rajiun. Ina yi wa mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari GCFR ta’ziyyar mutuwar Alhaji Ismaila Isa Funtua."
Tsohon gwamnan ya ce: "A matsayinsa na abokin tafiyar marigayin mahaifina, Alhaji Funtua ya kasance mani wani tafki na hikima.”
“A ko yaushe a shirye ya ke ya bani shawarwarinsa da ra’ayoyi game da batutuwa. Zan yi kewansa, Najeriya ta rasa ‘dan kishin kasa kuma ya kasance tambarin hadin-kai.”
“Ina mika ta’aziyya ta ga iyali, abokai, mutane da gwamnatin jihar Katsina da kuma kasa baki daya. Ubangiji Allah SWT ya gafarta masa, ya ba shi gida a Aljannah Firdaus.” Inji Saraki
Funtua ya rike ministan harkokin ruwa a gwamnatin Shagari, a lokacin mahaifin Saraki watau Marigayi Olusola Saraki shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng