Buhari: Mutuwar Ismail Funtua ta bar mani babban gibi domin ya kasance tare da ni

Buhari: Mutuwar Ismail Funtua ta bar mani babban gibi domin ya kasance tare da ni

A ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, 2020 ne aka samu labari bagatatanwastam cewa Malam Isma’ila Isa Funtua ya rasu bayan ya samu bugun zuciya.

Isma’ila Isa Funtua ya na cikin manyan na-hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma surukinsa ne bayan abokantakar da ke tsakaninsu.

Shugaban kasar ya yi jawabi ta bakin Garba Shehu ya na nuna takaicin wannan rashi, inda ya aika sakon ta’aziyya ga ‘yanuwan marigayin da kuma mutanen Katsina.

“Cikin takaici, shugaba Muhammadu Buhari ya samu labarin mutuwar tsohon abokinsa kuma na kusa da shi, Malam Isma’ila Isa Funtua, wanda ya kasance shugaba ne na kungiyar NPAN.”

Jawabin ya kara da cewa:

“Shugaban kasar ya na yi wa iyalai da dangi, da gwamnati da kuma mutanen jihar Katsina da abokai da na-kusa da tsohon shugaban na NPAN, musamman abokansa a harkar aikin jarida ta’aziyyar wannan rashi.”

KU KARANTA: Sama Isa ya mutu

Buhari: Mutuwar Ismail Funtua ta bar mani babban gibi domin ya kasance tare da ni
Marigayi Ismail Funtua
Asali: Twitter

Buhari ya bayyana marigayin da “Mutumin da ake kauna kuma ake ganin darajarsa.”

“Shugaba Buhari ya yi imani cewa mutuwar ‘dan jaridar kuma ‘dan kasuwar ya kirkiri wani wawakeken gibi domn Malam Funtua ya kasance a kullum tare da shi a tafiyarsa ta siyasa.”

Tsohon ministan kasar ya kasance wadanda su ka rika dafawa Muhammadu Buhari har ya kai ga zama shugaban kasar Najeriya bayan shekaru fiye da goma ya na harin kujerar.

“Shugaban kasar ya roki Allah ya karbi Malam Funtua, sannan ya ba iyalinsa juriya da ikon jure wannan rashi.” Inji Shehu, mai magana da yawun shugaba Buhari.

Funtua ya rasu ne kwanaki kimanin 93 bayan aminin shugaban kasa kuma babban hadiminsa watau Abba Kyari ya cika. Funtua mutumin jihar Katsina ne kamar shugaban kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel