Mai nakasa ya bayyana hoton satifiket dinsa bayan ya kammala NYSC

Mai nakasa ya bayyana hoton satifiket dinsa bayan ya kammala NYSC

- Wani mai fama da nakasa ya yi dacen kammala aikin bautar kasa a Najeriya

- Eboghoye Emmanuel Eboseremhen ya karbi shaidar satifiket daga hukumar NYSC

- Wannan Bawan Allah ya yi amfani da shafinsa na Instagram ya wallafa hotonsa

Wani mai fama da larurar gurgunta ya ba mutane mamaki bayan da ya wallafa hotonsa dauke da takardar shaidar kammala hidimar kasa watau NYSC.

Matashin mai suna Eboghoye Emmanuel Eboseremhen ya na cikin rukunin sahu na biyu watau Batch ‘B’ wanda aka yaye daga aikin bautar kasa a makon da ya gabata.

A ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2020, hukumar NYSC ta fara rabon takardun satifiket ga wadanda su ka kammala shirin, za a dauki kwanaki goma ana wannan aiki.

A daidai wannan lokaci ya zama al’adar matasa da su ka yi bankwana da bautar kasa a garuruwa da-dama su rika bayyana hotonsu dauke da takardun shaidarsu.

Ba a bar Eboghoye Emmanuel Eboseremhen a baya ba, domin shi ma ya dauki hotonsa rike da na shi satifiket din ya na mai tsaye a kan gwiwowinsa.

KU KARANTA: Mutane 5 sun bata diyar wani gurgu a Kaduna

Mista Eboghoye Eboseremhen gurgu ne wanda ba zai iya tafiya da kafafunsa ba. Duk da haka wannan bai hana shi zuwa makaranta har zuwa matakin gaba da sakandare ba.

Kamar yadda Eboghoye Eboseremhen ya nuna a shafinsa na Instagram, shi din kirista ne wanda ya yi Imani da Yesu a matsayin Ubangijinsa.

Da ya ke jawabi a shafin sada zumuntan, matashin ya rubuta: “Abin da na ke bauta shi ne rayayyen ubangiji. Ko shaidan ya san da haka. Ina bautar Ubangiji rayayye.”

Ya kara da cewa: “Kowa ya san kai ne ka ke mulkin Duniya. Yesu!” - @Eboghoye_emmanuel_eboseremhen

Jama’a da dama sun fito su na taya wannan Bawan Allah murnar cin ma wannan mataki a rayuwa.

Ana rade-radin cewa Mista Eboseremhen ya yi karatun digiri ne a jami’ar Ambrose Ali da ke garin Ekpoma, jihar Edo, inda ya karanta ilmin kimiyyar siyasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel