Da duminsa: Lauyan Magu ya bayyana abinda suke tsammani daga kwamitin bincike

Da duminsa: Lauyan Magu ya bayyana abinda suke tsammani daga kwamitin bincike

- Lauyan tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu, Wahab Shittu, ya mayar martani ga kan furucin kakakin shugaban kasa, Garba Shehu

- Shittu ya ce wanda yake karewa na tsammanin abun mamaki amma na alkhairi daga kwamitin fadar shugaban kasar a kan zargin da ake masa

- Ya kara da cewa, wanda yake karewar zai mika takardun bayanan kariyarsa ga kwamitin

Lauyan dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, Wahab Shittu, ya ce wanda yake karewa na tsammanin abun mamaki amma na alkhairi daga kwamitin fadar shugaban kasar a kan zargin da ake masa.

Shittu ya sanar da hakan ne a ranar Litinin a wani martani da yayi a kan maganar mataimaki na musamman ga shugaban kasa a fannin yada labarai, Garba Shehu.

Shehu dai ya yi wata hira ne da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, kan lamarin.

Da duminsa: Lauyan Magu ya bayyana abinda suke tsammani daga kwamitin bincike
Da duminsa: Lauyan Magu ya bayyana abinda suke tsammani daga kwamitin bincike Hoto: The Cable
Asali: UGC

Da yake amsa tambaya a kan ikirarin lauyan Magu, na cewar binciken mayyar-farauta ce Shehu ya ce: "Ina tunanin wannan tambayar ta kwamitin Ayo Salami kuma zan iya cewa kwamitin ya tara jama'a masu nagarta a fadin kasar nan kuma za su yi abinda ya dace.

"Ba zan ce komai game da kwamitin ba amma ina shawartar 'yan Najeriya da su tsammaci abun mamaki zuwa lokacin da suka gama aikinsu. Ku shirya ganin abun mamaki."

A wata tattaunawa da jaridar Vanguard tayi da Shehu, Shittu ya ce ababen mamakin da za su zo daga kwamitin za su kasance na alkhairi.

Ya ce: "Muna nan muna tsammanin alheri. Alheri ne zai zo wa wanda muke karewa."

Shittu ya kara da cewa, wanda yake karewar zai mika takardun bayanan kariyarsa ga kwamitin.

A wani labarin kuma, Buba Galadima, ya ce tsige Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), da aka yi duk farfaganda ce.

Buhari ya nada Mohammed Umar, tsohon daraktan ayyuka na EFCC, a matsayin mukaddashin shugaban hukumar bayan dakatar da Magu.

A wata hira da jaridar The Sun, Galadima ya ce maye gurbin Magu da wani shine ake kira da an ci moriyar ganga aka kuma ya da koronta.

Ya yi zargin cewa Magu na ta bin umurnin wasu masu mulki a gwamnati mai ci amma ya take wasu wanda hakan ne ya yi sanadiyar dakatar da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng