Ana zargin maza 5 da laifin amfani da karamar yarinya a Jihar Kaduna

Ana zargin maza 5 da laifin amfani da karamar yarinya a Jihar Kaduna

Jaridar Daily Trust ta ce matasan karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna sun ceci yarinya mai shekara 10 da haihuwa da wasu maza biyar su ke kwanciya da ita.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin wadanda su ke lalata da wannan karamar yarinya har da mijin goggonta. Mahaifin yarinyar nakasasshe ne wanda ba ya iya motsi.

Yanzu wannan yarinya da aka nemi a lalatawa rayuwa ta na karkashin kulawar Hajiya Rabi Salisu ta kungiyar Arida Foundation of Nigeria (AFN).

Rabi Salisu wanda ta fito a wani bidiyo da yanzu ya zagaye Duniya dauke da yarinyar ta bayyana cewa mahaifiyar yarinyar sun rabu da mahaifinta.

Salisu ta ke cewa yarinyar ta samu kanta a cikin wannan hali ne bayan mahaifiyarta ta kai ta kara wajen mijin ‘yar uwarta saboda ba ta zuwa talla idan aka tura ta.

Wannan Bawan Allah ya yi amfani da damar da ya samu na kwabar yarinyar, ya kare da kawo wasu ‘yanuwansa har maza biyu wanda su ka rika lalata da yarinyar.

Daga baya wannan Baiwar Allah ta kai kuka wajen mahaifiyarta cewa ta na ganin jini idan ta yi bawali. Daga nan ne tsohuwarta ta ja-kunnen mijin yayartan da ya yi nesa da diyarta.

KU KARANTA: Masu fyade sun yi sanadiyyar mutuwar wata yarinya

Ana zargin maza 5 da laifin amfani da karamar yarinya a Jihar Kaduna
Ministar harkokin mata a Najeriya
Asali: UGC

“Bayan ta koma ta cigaba da talla, sai kuma ta hadu da wani mutumi mai saida gwanjo, wanda ya saya mata takalmin makaranta, ya rika yin lalata da ita.”

“Daga nan kuma sai wani mutumi mai gidan burodi ya shiga sahu, bayan ya saye shinkafar da ta ke saidawa.”

“A karshe an samu maza kusan biyar su na biyan bukatarsu da wannan yarinya.”

Da manema labarai su ka tuntubi Rabi Salisu, ta ce yanzu ana kula da yarinyar sakamakon cututtukan da ta kamu da su, da kuma wasu rauni a bangaren al’aurarta.

Kawo yanzu shugabar kungiyar ta AFN ta bayyana cewa an kama mutum hudu daga cikin wanda ake zargi, ana cigaba da bincike domin a gurfanar da su.

Kakakin ‘Yan sanda na Kaduna ASP Mohammed Jalige, ya ce mutane biyu daga ciki sun amsa laifinsu, sauran biyun ba su kai ga amsa laifin na su ba, sannan ana neman guda.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel