Da dumi - dumi: Shugaban kwamitin binciken badakalar NDDC ya yi murabus

Da dumi - dumi: Shugaban kwamitin binciken badakalar NDDC ya yi murabus

Shugaban kwamitin majalisar wakilai da ke binciken badakalar kudi a hukumar kula da cigaban yakin Neja - Delta (NDDC), Honarabul Olabunmi Tunji - Ojo, ya sauka daga mukaminsa.

A makon jiya ne kwamitin majalisar ya fara gayyatar tsofin shugabanni da ma su ci yanzu a hukumar NDDC domin amsa tambayoyi a kan badakalar da ake zargin ana tafkawa a hukumar.

A ranar Alhamis din makon jiya ne mukaddashin shugaban NDDC, Daniel Pondei, ya jagoranci mukarrabansa wajen ficewa daga dakin da kwamitin majalisa ke yi ma sa tambayoyi a kan zargin badakala a hukumar.

Honarabul Tunji - Ojo, ya sanar da yin murabus dinsa ne ranar Litinin yayin zaman kwamitin domin cigaba da gudanar da binciken badakala a hukumar NDDC.

Murabus din dan majalisar ba zata rasa nasaba da zarginsa da cin hanci da Mista Pondei ya yi ba a makon jiya.

Da ya ke bayyana dalilinsa na ficewa daga wurin zaman kwamitin bincike da majalisa ta kafa, Mista Pondei ya bayyana cewa ba zai yi magana a gaban kwamitin da ake zargin shugabansa da cin hanci ba.

Sauran mambobin kwamitin sun bayyana amincewarsu da shugabancin Honarabul Tuni - Oyo. Kazalika, sun bukaci Mista Pondei da ministan yankin Neja - Delta, Sanata Godswill Akpabio, su bayyana a gaban kwamitin ranar Litinin, 20 ga watan Yuli.

Da dumi - dumi: Shugaban kwamitin binciken badakalar NDDC ya yi murabus
Shugaban kwamitin binciken badakalar NDDC yayin fita daga zauren da suke zama bayan sanar da yin murabus
Asali: Twitter

Har ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoton, ministan da shugaban NDDC suna zaune a gaban kwamitin domin fara amsa tambayoyi.

Da ya ke magana a kan dalilinsa na yin murabus, Honarabul Tunji-Ojo ya ce ya yanke shawarar yin hakan ne domin bawa kowanne bangare sukunin bayyana kansa ba tare da wata togaciya ba.

Daga ranar Alhamis ne binciken da akeyi na badakalar hukumar NDDC ya kara daukar zafi inda jami'an rundunar 'yan sanda suka mamaye gidan tsohuwar mukaddashiyar daraktan hukumar bunkasa Niger Delta, Joy Nunieh, da ke Fatakwal.

DUBA WANNAN: FG ta fara gwajin sabbin jiragen kasa da ta sayo daga China (Bidiyo)

Akwai zargin da akeyi na cewar 'yan sandan sun mamaye gidan Nunieh ne domin hanata barin Fatakwal zuwa Abuja inda zata fayyace gaskiya gaban kwamitin binciken.

A baya bayan nan, Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktar hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta (NDDC), ta zargi Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta da damfara.

Nunieh ta zanta da manema labarai bayan bayyana da tayi a gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar dattawa a kan bincikar NDDC.

Ta zargi cewa, Akpabio ya bukaceta da ta canja dalolin da ke asusun bankin NDDC zuwa naira, ta kori shugaban tawagar lauyoyin hukumar wanda dan arewa ne.

Sannan cewa ta cire dukkan daraktocin da suka ki bin umarninsa tare da yi wa Peter Nwaoboshi sharri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel