Kyau yankin Kudu su karbi mulkin kasar nan a 2023 - Adebanjo, Yakassai, Clark

Kyau yankin Kudu su karbi mulkin kasar nan a 2023 - Adebanjo, Yakassai, Clark

A yayin da aka fara harin kujerar shugaban kasa, jaridar Vanguard ta rahoto wasu fitattun ‘yan Najeriya sun fito su na kiran a tsaida shugaban kasa a 2023 daga yankin Kudancin kasar.

Daga cikin masu wannan magana akwai Alhaji Tanko Yakassai, Cif Edwin Clark, Cif Ayo Adebanjo; Janar Idris Dambazzau, mai ritaya, Idongesit Nkanga, da sauransu.

Har irinsu Dr. Junaid Mohammed, Bode George, Ebenezer Babatope, Supo Shonibare da Femi Okorounmu su na da wannan ra’ayi. Ana kuma ganin Kudu maso gabas ya fi dacewa da mulkin.

Tsohon ‘dan siyasar jamhuriya ta farko, Alhaji Tanko Yakassai ya ce: “Ware mulki zuwa wani yanki ba doka ba ce, tsari ne na ‘yan jam’iyya, ba ya cikin kundin tsarin mulki.”

Yakassai ya ke cewa: “Ya ragewa ‘yan jam’iyya su zabi inda su ke so ‘dan takarar su ya fito.”

Idris Bello Dambazzau, wanda ya na cikin manyan APC a Kano, ya na tare da Yakkasai, ya ce:

“Kudu maso yamma su fito da shugaban kasa saboda gwamnatin APC hadaka ce tsakanin Arewa maso yamma, Arewa maso gabas, Kudu maso yamma da wani bangaren tsakiyar Najeriya.”

KU KARANTA: Babu abin da zai hana Tinubu mulki a 2023 - Yaran Tinubu

Kyau yankin Kudu su karbi mulkin kasar nan a 2023 - Adebanjo, Yakassai, Clark
Alhaj Tanko Yakassai
Asali: UGC

Shugaban kungiyar Afenifere chieftain, Pa Ayo Adebanjo cewa ya yi: “Mulki ya tafi Kudu, babu tantama a kan wannan. Mu daina yaudarar kanmu. Kudu su ka dace da mulki.”

Shi ma wani jagora a tafiyar Afenifere, Supo Shonibare, cewa ya yi fito da shugaban kasa daga yankin Kudu shi ne abin da ya fi dacewa, amma kafin nan ayi wa tsarin kasar garambawul.

Shugaban PANDEF ta Neja Delta, Nkanga ya ce: “Matsayarmu ita ce idan akwai yarjejeniya tsakanin Arewa da Kudu, to idan mulki zai zo Kudu, yankin Kudu maso gabas ya fi dacewa.”

Da alama gardamar ta na ga wani yanki ne zai tsaida ‘dan takara. Tsohon Ministan sufuri, Cif Ebenezer Babatope, ya ce Kudu maso gabas ne ya kamata su fito da shugaba a 2023.

Shi kuma Dr. Junaid Mohammed ya nuna ya fi damuwa da tsarin da zai fito da ‘dan takarar da ya fi cancanta a maimakon ayi ta kwakwazo a kan yankin da za su kawo shugaban kasar.

“Zaman lafiyar kasar nan shi ne Kudu da Arewa su rika yin kama-kama a mulki, don haka bayan shugaban kasa Buhari ya kammala shekaru takwas, sai yankin Kudu su karba.” Inji Edwin Clark.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel