Garba Shehu ya mayarwa da 'yan adawa martani a kan zargin karbe akalar mulkin Najeriya daga hannun Buhari

Garba Shehu ya mayarwa da 'yan adawa martani a kan zargin karbe akalar mulkin Najeriya daga hannun Buhari

Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya ce har yanzu cikakken ikon sarrafa akalar mulkin Najeriya ya na hannun shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin wani jawabi da ya fitar domin mayar da martani ga ma su zargin cewa shugaba Buhari ya zama dan kallo a harkar mulkin kasa, Garba Shehu ya ce ma su fadin haka sun biyewa rudun 'yan adawa.

Kakakin ya zargi jam'iyyun hamayya da 'yan adawa da yada karyar cewa "ba shugaba Buhari ne ke sarrafa akalar al'amuran gwamnatinsa ba.

Ya bayyana cewa duk da 'yan Najeriya za su iya fahimtar gwamnati ta hanyoyi da bangarori daban - daban, akwai wadanda ke kalaman batanci ga gwamnati mai ci "bayan sun shafe shekaru 16 a gwamnati babu abinda suke yi sai rura wutar cin hanci."

"Akwai bukatar fadar shugaban kasa ta mayar da martani a kan rahotannin wasu jaridu da aka wallafa ranar Lahadi, wadanda ke nuna cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bashi da iko da gwamnatinsa.

"Wasu daga cikin ma su wallafa irin wadannan rahotanni suna fakewa da sunan adawa mai muhimmanci, yayin da wasu ke biyewa rudu irin na jam'iyyar adawa wacce ta shafe shekaru 16 ta na tafka cin hanci.

"A wasu lokutan mu kan yi mamakin yadda wasu kafafen yada labarai ke fitar da rahoto ba tare da yin la'akari da nauyin kalmomin da suke amfani da su wajen bayyana hujjojinsu ba.

Garba Shehu ya mayarwa da 'yan adawa martani a kan zargin karbe akalar mulkin Najeriya daga hannun Buhari
Garba Shehu
Asali: UGC

"To amma, gwamnati ta kawar da kai daga irin wadannan rahotanni marasa tushe domin tabbatarwa da duniya cewa a yanzu akwai 'yancin fadar albarkacin baki a kasa.

DUBA WANNAN: FG ta fara gwajin sabbin jiragen kasa da ta sayo daga China (Bidiyo)

"Babu laifin 'yan Najeriya su bayyana mabanbantan ra'ayi a kan binciken Ibrahim Magu, Godswill Akpabio, NDDC, NSITF da sauransu.

"Amma, babban abin damuwar shine yadda irin wadannan rahotanni ke fakewa da sunan adawa mai amfani wajen bayyana ra'ayin jam'iyyar siyasa da ta shafe shekaru 16 a gwamnati babu wani aiki sai daurewa cin hanci da rashawa gindi," a cewar Garba Shehu.

Garba Shehu ya kara da cewa zai zama tamkar cin amanar 'yan Najeriya idan gwamnatin shugaba Buhari ta ki yakar cin hanci, a saboda haka 'yan Najeriya su gyara zamansu domin zasu sha mamaki in dai maganar yaki da cin hanci ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng