Yanzu-yanzu: NAF ta bayyana wanda ya kashe Arotile, ta mika lamarin ga ‘yan sanda

Yanzu-yanzu: NAF ta bayyana wanda ya kashe Arotile, ta mika lamarin ga ‘yan sanda

Rundunar sojin saman Najeriya a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuli, ta bayyana direban motan da ya bige marigayiya Tolulope Arotile, matukiyar jirgin yakinta.

Daraktan yada labarai na rundunar, Ibikunke Daramola, ya bayyana hakan bayan kammala wani taro a Abuja.

Daramola ya bada sunan tsohon dan ajin su Arotile da ya kasheta a matsayin Nehemiah Adejoh.

Kakakin NAF ya kara da cewa za a mika al'amarin ga 'yan sandan Najeriya saboda na ya shafi farar hula.

Ya ce an mika wannan bayanin ga 'yan uwan matukiyar jirgin wadanda ke ci gaba da makokinta.

A yayin bada rahoton binciken farko da NAF tayi, kakakin ya ce marigayiya Arotile ta hadu da tsoffin 'yan ajinsu a makarantar sakandire a ranar da abun ya faru.

Yanzu-yanzu: NAF ta bayyana wanda ya kashe Arotile, ta mika lamarin ga ‘yan sanda
Yanzu-yanzu: NAF ta bayyana wanda ya kashe Arotile, ta mika lamarin ga ‘yan sanda Hoto: Fresh FM
Asali: UGC

Ya ce, "Nehemiah Adejoh, Igbekele Folorunsho da Festus Gbayegun sun wuce ta a wata mota kirar Kia Sorrento SUV da lambar rijista AZ 478 MKA.

"Dukkan su ukun farar hula ne kuma suna rayuwa ne a wajen barikin cikin Kaduna amma suna kan hanyarsu ta zuwa wurin wata Chioma Ugwu, matar Squadron Leader Chukwuemeka Ugwu wacce ke zama a kwatas din Ekagbo.

"Bayan gane 'yar ajinsu Arotile, Adejoh da ke tuki ya koma baya da motar don samunta. Motar ta bigeta inda kanta ya bugu a kasa. Motar ta hau wani sashi na jikinta wanda hakan yasa ta samu raunika."

Daramola ya ce an gaggauta mika Arotile asibiti amma wurin karfe 4:45 na yamma aka tabbatar da mutuwarta.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi wa sojojin Najeriya kwanton bauna, sun kashe 16 a Katsina

Ya yi bayanin cewa a take aka kama 'yan ajin nasu inda aka yi musu gwajin giya amma babu wani nau'i a tattare da su.

"Sai dai an gano cewa direban motan, Mista Nehemiah Adejoh, bai da lasisin tuki mai aiki.

"Kasancewar lamari da ya shafi farar hula ne, za a mika shi ga rundunar 'yan sandan Najeriya domin ci gaba da binccike da kuma mika wadanda ake zargin a kotu kamar yadda doka ta tanadar," in ji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel